✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harkokin Noma: Saminaka ce kan gaba a Afirka ta Yamma – Sanata

Kamfanin irin shuka na Mashala dake tallafawa manoma da rancen irin shuka da takin zamani ya shirya ranar manoma a wata babbar gona dake kauyen…

Kamfanin irin shuka na Mashala dake tallafawa manoma da rancen irin shuka da takin zamani ya shirya ranar manoma a wata babbar gona dake kauyen Gidan Dutse a karamar Hukumar Lere dake Jihar Kaduna.

Da yake jawabi a wajen taron, Mai Martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya bayyana cewa aikin noma ne kadai zai inganta Najeriya da kasashen Afrika baki daya.

Ya ce babu abin da zai taimaki talakan Najeriya kamar noma, kuma babu wani taimako da za a yi wa manoman kamar samar masu da irin shuka ingantatce da kuma takin zamani kan farashi mai rahusa.

Ya ce babu shakka al’ummar karamar Hukumar Lere sun rungumi aikin noma musamman noman masara, don haka yankin ya shahara a duniya. Sai kuma ya yabawa wannan kamfani na Maslaha kan yadda yake samarwa da manoma irin shuka ingantatce.

“Wannan kamfani ya yi rawar gani a Najeriya da kasashen Afrika wajen samarwa da manoma ingantatcen irin shuka. Don haka muna godiya ga wannan kamfani kuma muna tabbatarwa kamfanin cewa zamu cigaba da rike shi. Domin irin masarar da ya kawo Lere zai taimaka wajen bunkasa noman masara a  yankin da ma Jihar Kaduna da kasa baki daya”.

Shi ma a nasa jawabin, wani babban manomi a yankin da aka yi wannan biki a gonarsa, Alhaji Abdul’azeez Gidan Dutse ya bayyana cewa yana da manyan gonaki 12, amma ada noman ya so gagararsa. Ya ce amma da taimakon Allah da Ya kawo wannan kamfani a daminar bana, suka ba shi irin masara da takin zamani ya yi noman da bai taba yin irinsa ba, wajen yawa da kyau. “Wannan gona da ake yin wannan biki a cikinta ada ina sanya mata buhunan taki 300 amma a daminar bana na sanya mata taki buhu 125 kawai, saboda amfani da na yi da irin shuka na wannan kamfani,” in ji shi.

Tun da farko shugaban kamfanin na Maslaha Seeds, Sanata Saidu Muhammad Dansadau ya bayyana cewa babban burin wannan kamfani shi ne bunkasa harkokin noma a Najeriya, domin a bunkasa kasar da abinci da wadata masana’antu da kayayyakin amfanin gonar da zasu rika sarrafawa da kuma daukar masarar da manoma suka noma a fitar zuwa kasashen waje.

Ya ce wannan kamfani shi ne na daya a Afrika ta Yamma wajen samar da ingantatcen irin shuka. “kwararru kan aikin noma sun tabbatar da cewa yankin Saminaka ne kan gaba a aikin noma a Afirka ta yamma. Don haka wannan kamfani ya zo yankin domin ya yi aiki tare da manoman wajen bunkasa harkokin noma a Najeriya.”

Haka zalika wakilin kamfanin a karamar Hukumar Lere, Alhaji Umaru Haidanu Ibrahim Saminaka ya bayyana cewa, manoman wannan yanki sun yi amfani da eka dubu 4 ne na wannan shiri a daminar bana. Ya ce a cikin manoman da suka shiga wannan shiri akwai manoman da aka baiwa taki tirela uku da buhu 124 rance, da wadanda aka baiwa taki tirela biyu, da wanda aka baiwa taki tirela daya.