Akalla mutum 16 sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu hudu suka jikkata sakamakon harin da mayakan Boko Haram suka kai a Karamar Hukumar Geidam ta Jihar Yobe.
Bayanai sun ce mayakan sun yi wa kauyen Nguru Kayayya dirar mikiya ne da misalin karfe 9:00 safiyar ranar Litinin yayin da galibin mazauna yankin ba su farka daga barci ba.
- CBN ya musanta yunƙurin ƙirƙirar sabbin takardun Naira a baɗi
- Kare rayuka da mutunta ayyukan jin kai a Gaza ya zama wajibi — MDD
Wata majiya da ke da makusanta a garin da lamarin ya faru, ta shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa ta kidaya gawarwaki 16 wanda galibinsu matasa ne.
“Sun kai wa garin harin ne yayin da galibin mazaunansa ke barci.
“Na ziyarci garin da kaina kuma na kidaya gawarwaki 16 yayin da wasu mutum hudu sun jikkata.
“A halin yanzu wadanda suka ji raunin suna karɓar magani a Asibitin Geidam.
Majiyar ta ce ’yan ta’addan sun kai wa kauyen hari ne bayan mazaunansa wadanda galibi manoma ne sun ƙi biyan harajin da mayakan suka ɗora musu.
“Mazauna kauyen sun shaida min cewa mayakan sun ɗora musu haraji, amma saboda sun bijire wa umarnin ya sanya suka kawo musu hari.
“Lamarin dai ya sanya mutane da dama sun tsere zuwa wasu wuraren a Karamar Hukumar Geidam domin neman mafaka,” in ji shi.
Yayin da yake tabbatar da lamarin, wani mai fafutika kare hakkin dan Adam, Babagana Aisami Geidam, ya ce mutum 16 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon harin.
Kazalika, ya ce akwai wasu mutum uku da suka jikkata yayin da wani mutum daya ke yanayi na rai-kwakwai-mutu-kwakwai.
Tuni dai an binne gawarwakin mutum 16 da suka riga mu gidan gaskiya yayin da jami’an soji suka dira a kauyen da lamarin ya shafa.
Mai magana da yawun rundunar Operation Lafiya Dole, Kyaftin Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce maharan sun yi ikirarin cewa mazauna kauyen suna bai wa sojoji bayanai da ke taimaka musu yi wa maboyarsu tarnaki.
“Ba zan iya bayar da hakikanin alkalumman asarar rayukan da aka samu ba, amma dai an tura dakaru zuwa kauyen da lamarin ya faru domin kwantar da tarzoma,” in ji shi.