A wani aikin hadin gwiwa na dakarun soji da jami’an ’yan sanda, an samu nasarar dakile wani mummunan harin ’yan daban daji a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Hukomomin biyu a ranar Juma’a sun dakile harin da ’yan daban daji suka yi yunkurin kai wa matafiya a kan babbar hanyar da miyagu suka saba cin karensu babu babbaka.
Wakilanmu sun tabbatar da cewa babu ran ko mutum daya da ya salwanta sai dai matafiya kalilan da wani jami’an tsaro sun samu rauni kankani.
- Jerin kasashe da Saudiyya ta gindaya wa sharadin shiga cikinta
- Najeriya ta karbi rigakafin COVID-19 daga Rasha
Gwamnatin Jihar Kaduna ta bakin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan, ta tabbatar da aukuwar wannan lamari.
Aruwan yayin zantawa da manema labarai ya sanar cewa jami’an tsaro sun dakile harin ne yayin da ’yan ta’addan suka bude wuta a kan matafiya daura da Kamfanin Olam Feeds da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufa’i ya yaba wa jarumtar da jami’an tsaron suka nuna tare da addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.