Shalkwatar Tsaro ta Kasa ta ce hare-haren dakarun Rundunar Tsaro ta Operation Lafiya Dole ya karkashe ‘yan ta’addan Boko Haram da dama a maboyarsu dake Njima da Dure a dajin Sambisa dake jihar Borno.
Jami’in sashen dake samar da bayanai kan ayyukan rundunar, Manjo Janar John Enenche ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis.
- An ba da damar shan giya da zina bayan yi wa Shari’ar Musulunci kwaskwarima a UAE
- ‘Azaba ce ta sa suka amsa laifin Boko Haram a Dubai’
Ya ce rundunar na ci gaba da samun gagarumar nasara a yakin da take yi da ‘yan ta’addan a yankin Arewa maso Gabas.
Manjo Janar Enenche ya ce sun kai harin na baya-bayan nan ne ranar Talata bayan jiragensu na sama sun gano maboyar ‘yan ta’addan a wuraren guda biyu.
A cewarsa, jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya sun tarwatsa maboyar mayakan kungiyar tare da yi musu barna mai yawan gaske.
“Rundunar Sojoji ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yakin da take yi har sai ta kakkabe dukkan ‘yan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da suke fama da rikici,” inji Enenche.