✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Mauludi: Gwamnatin Kaduna ta sa a yi bincike

Gwamna Uba Sani ya ba da umarnin bincike kan harin bom din jirgin sojin da ya kashe mutane akalla 80 a taron Mauludi a jihar.

Gwamman Kaduna, Uba Sani ya ba da umarnin yin bincike kan kisan mutane akalla 80 a harin bom din da wani jirgin sojoji ya kai wa masu taron Mauludi a jihar.

Wasu mazauna sun ce yawan wadanda suka rasu ya kai 90, wasu da dama kuma sun ji rauni a sakamon hare-haren bom da jirgi mara matuki na rundunar sojin kasa ta Najeirya ya kai wa taron Mauludin a yankin Tudun Biri.

Wasu mazauna garin da suka tsallake rijiya da baya a harin sun shaida wa Aminiya cewa suna tsaka da taron Mauludin ne suka ga jirgi yana shawagi, kafin su ankara ya jefo musu bom har sau biyu.

Wani mazaunin yankin mai suna Liman ya ce sun binne sama da mutum 90, da suka hada da mata biyu da ’ya’yan wani magidanci.

Shi ma wani wanda ya sha da kyar a harin, Bello Shehu Gara, “Muna cikin bikin Maulidi ne sai muka hangi jirgin na shawagi a sama, kafin mu ankara sai kurum ya sako bom wanda ya halaka mutum kusan 57.

“Sai muka hangi wasu na neman taimako, mun kai masu dauki, kurum sai jirgin ya sake sako wani bam din, daga Nan muka gudu,” inji shi

Ya ce sun yi jana’izar mutum akalla 74 da safiyar Litinin, banda gawarwakin da aka zuba a cikin buhu aka binne.

Uba Sani ya ba da umarnin bincike

Gwamna Uba Sani ya bayyana damuwa da irin girman barnar da harin bom din ya yi, yana mai cewa ya zama wajibi a gudanar da bincike.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta bayyana cewa wani jirginta mara matuki ne ya kai wa masu Mauludin hare-haren a bisa kuskure a daren ranar Lahadi, a yayin da yake sintirin yaki da ’yan ta’dda.

Da yake bayani kan lamarin, Uba Sani ya jajanta wa wadana abin ya shafa, ya kara da cewa yin bincike ya zama wajibi domin kauce wa faruwar irin hakan a nan gaba.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki nauyin kudin asibitin duk wadanda suka samu rauni a sakamakon harin.

Ya kara da cewa tuni aka kwashe su zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko inda suke samun kulawa.