Akalla mutane 13 suka mutu bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wani gidan cin abinci da shaidu suka ce cike yake da jami’an gwamnatin da sauran ‘yan siyasa a yankin tsakiyar Kasar.
Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwaito cewa, tuni kungiyar al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin, da ya jikkata wasu mutane 18, baya ga rayukan da ya lakume a garin Beledweyne da ke tsakiyar kasar Somaliya a ranar Asabar.
- Kungiyoyin Arewa sun bukaci shugaban NNPC ya yi murabus
- Kar a biye wa PDP ko APC a Zaben 2023 —Kwankwaso
Cikin makonni biyun da suka gabata, sai da kungiyar ta Al Shebaab ta kai wasu hare-haren kashi biyu a sassan kasar Somalia.
Jami’an ‘yan sanda da na gwamnati sun tabbatar da harin kunar bakin waken da aka kai gidan cin abincin, amma ba su bayyana adadin wadanda suka mutu ba.