✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Jirgin Soji: Nan da makonni 2 za a fara sabunta gina Tudun Biri —Gwamnan Kaduna

Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya ce nan da makonni biyu za a fara aikin sake gina kauyen Tudun Biri, inda wani jirgin soja ya kai…

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya ce nan da makonni biyu za a fara aikin sake gina kauyen Tudun Biri, inda wani jirgin soja mara matuki ya kai hari bisa kuskure a ranar 3 ga Disamba, 2023.

Gwamna Uba Sani ya bayyana hakan ne a taron Kungiyar Fityanul Islam ta Najeriya, wanda aka gudanar a Jami’ar Jihar Kaduna ranar Asabar.

Uba Sani ya ce “Kwanaki biyar da suka gabata na gana da shugaban kasa kan bukatar a gaggauta sake gina Tudun Biri, inda ya kira mataimakinsa, muka tattauna, kuma (Tinubu) ya tabbatar min da cewa nan da makonni biyu za a fara aikin.”

Gwamnan ya ba da tabbacin za a gina gidaje, asibiti, makaranta, kasuwa, da ofishin ’yan sanda a Tudun Biri karkashin aikin na gwamnatin tarayya.

Ya kuma bayyana goyon bayan gwamnatin jihar, bayan da ta dauki nauyin jinyar mutane 75 da abin ya shafa a tsawon kwanaki 17 da aka kwantar da su a asibiti.

Kazalika ya sanar da kafa wani kwamiti karkashin jagorancin mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe domin raba tallafin da aka ba wa al’ummar garin gudunmmawa, ya kuma jaddada kudirin sana tabbatar da adalci wajen rabon.

Tun da farko, shugaban kungiyar Fityanul Islam na kasa Sheikh Muhammad Arabi Abdul Fathi ne ya bukaci gwamnati da ta gaggauta sake gina Tudun Biri.

 Shugaban kungiyar ya kuma kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba da tallafin kudin Hajjin 2024 saboda karin kudin canji.