Kimanin mutane dubu 45 suka rasa muhallansu a kasar Syria bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin mayakan IS da dakarun Kurdawa tsawon kwanaki uku.
An dai gwabza tsakanin bangarorin biyu a lokacin da kungiyar ta IS ta kaddamar da farmaki kan gidan Yarin Ghwayran a ranakun Alhamis zuwa Lahadin makon jiya.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum daya, sun sace 15 a Neja
- Yadda mutumin da ake tuhuma da kashe Hanifa ya gurfana a Kotu
A kasar Syria dai an shafe kwanaki uku ana gwabza kazamin fada tsakanin mayakan kungiyar ISIS da na Kurdawa, inda akalla mutum 70 aka kashe ya zuwa yanzu.
Fadan dai ya faro ne bayan wani hari da dakarun IS din suka kai wani gidan yarin da ke kunshe da mambobinsu kusan 3,500 a ciki.
Harin, wanda aka kai gidan yarin Ghwayran, shi ne irinsa mafi muni da kungiyar ta kai tun bayan da aka ayyana yin galaba a kanta, kimanin shekara uku da suka wuce.
“Akalla dai mayakan Kurdawa 28 da wasu fararen hula biyar da kuma mayakan ISIS 45 ne aka hallaka,” inji Rami Abdel Rahman, Shugaban wata cibiya ta Birtaniya da ke sa ido kan kare hakkin dan Adam a Syria.
Tun da fari mayakan na IS sun kai harin ne da nufin kubutar da mambobinsu da ke tsare a gidan Yarin mai matukar tsaro, lamarin da ya juye zuwa kazamin gumurzu da ya lakume rayukan mutane da dama.
Bayanai sun ce an dai sake kama daruruwan fursunonin daga bisani, amma har yanzu akwai wadanda suka cika wandonsu da iska.
Mayakan Kurdawan dai tare da goyon bayan jiragen yakin Amurka na can sun yi wa kurkukun kawanya, a kokarinsu na sake kwace iko da shi.