An samu karin akalla fursunoni 40 da suka koma gidan gyara hali da ke babban birnin Jihar Imo bayan tserewarsu.
Ya zuwa ranar Laraba, adadin fursunoni 82 ne suka koma gidan gyara halin da ke Owerri.
- Matsorata ne suka kai hari Shelkwatar ‘Yan sanda a Imo — Osinbajo
- De Bruyne ya sabunta kwantaraginsa a Manchester City
- Real Madrid ta lallasa Liverpool, Man City ta samu nasara a kan Dortmund
- Tambuwal ya gargadi shugannin kananan hukumomi kan matsalar tsaro
Fursunoni fiye da 1800 ne suka tsere bayan wasu bata gari sun fasa gidan yarin a ranar Litinin.
Aminiya ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga ne suka kai hari shelkwatar ‘yan sanda da ke Jihar tare da kone sashen da ake ajiye bayanan manyan laifuka, sannan suka saki wasu da ke daure.
Yayin ziyarar gani da ido kan ta’asar da Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya kai a ranar Talata, ya ce za a yafe wa duk fursunan da ya dawo gidan yarin don kansa.
A wata tattaunawa da Aminiya ta yi da Kakakin Hukumar Kula da Fursunonin Jihar Imo, Mista Joe Madugba, ya ce fursunonin sun fara dawo gidan yarin ne daga ranar Talata zuwa Laraba.
Kazalika, Mista Madugba ya ce suna sa ran wasu da dama za su iya dawowa gidan yarin.