Babban Ofishin Tsaro ya ba da sanarwar sake damke wasu mutum biyu da ake zargin da hannunsu a harin da aka kai Mujami’ar St Francis Catholic da ke Owo a Jihar Ondo ran 5 ga watan Yuni.
Cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis, Daraktan Yada Labarai na ofishin, Manjo-Janar Jimmy Akpor, ya ce an kama wadanda ake zargin ne ranar Talata a yankin Omialafara (Omulafa), Ose, Jihar Ondo.
- Bayan fitowa da gidan yari, Dariye zai yi takarar Sanata
- Jirgin yaki ya kashe kasurgumin dan bindiga Alhaji Shanono da yaransa 18
Akpor ya ce kamen ya zo ne sa’o’i hudu bayan da Shugaban Rundunar Tsaro, Janar Lucky Irabor ya ba da sanarwar cafke hudu daga cikin maharan.
Ya kara da cewa, an damke wadanda ake zargin ne ta hadin gwiwa tsakanin sojoji da jami’an hukumar DSS.
A cewarsa, yana da kyau a fahimci cewa daya daga cikin wadanda aka cafke sun yi hadin gwiwa da ISWAP a baya sun jagoranci kai hari kan sojoji a yankin Okene, Jihar Kogi, wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka.
Jami’in ya ce burin shugabancin tsaron shi ne aiki tare tsakanin hukumomin tsaron da ake da su wajen yaki da matsalolin tsaron da kasa ke fuskanta domin maido da zaman lafiya.
(NAN)