Wani harin bam a masallaci ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutum 12 a yayin da suke sallah a kasar Afghanistan.
’Yan sandan Afghanistan sun ce harin ya kawo karshen kwana ukun da kungiyar Taliban ta bayar na tsagaita wuta don murnar Sallah Karama.
- Tsohon Shugaban Kasa IBB tsohon saurayina ne —Ummi Zee-zee
- Matashi ya rasu a garin gyaran lantarki a Kano
- Dala 65m: ICPC na neman surikin Buhari ruwa a jallo
- Tsawa ta kashe giwaye 18 a Indiya
Cikin mutane biyun da suka mutu har da limamin masallacin, wasu 15 kuma suka samu rauni.
Da take jawabi jami’ar yada labaran rundunar ’yan sandan yankin Shakar Darah, Ferdaws Framurz, ta ce ’yan ta’addan sun kai harin bam ne cikin masllacin ne a daidai lokacin da ake tsaka da yin Sallah.
Wannan hari dai shi ne na farko tun bayan da mayakan Taliban sun ba da sanarwar tsagaita wuta na kwana uku saboda bai wa jama’a damar gudanar da bikin Sallah Karama cikin kwanciyar hankali.
Afghanistan, na daga cikin kasashen da ke fuskantar yake-yake, tun bayan ficewar dakarun sojin kasar Amurka daga kasar.
Gwamnatin kasar ta shafe sama da shekara 10 tana yaki tsakaninta da Taliban, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.