Akalla mutum 41 ne suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon tashin bam yayin sallar Juma’a a masallacin Kandahar da ke Afghanistan.
Kungiyar Taliban wacce a bayan nan ta kwace ikon kasar ta tabbatar da cewa harin na kunar bakin wake ne wanda ya jikkatar da mutum 74.
Wannan hari na zuwa mako guda bayan aukuwar makamancinsa a Arewacin birnin Kunduz wanda kungiyar IS ta dauki alhakin kaiwa.
Hotunan cikin masallacin na Iman Bargah sun nuna yadda tagogi suka farfashe sannan ga gawarwaki a zube birjik a kasa da kuma wasu masu ibadar da ke kokarin taimakon wadanda suka jikkata.
Wani jami’in Taliban da ke kula da tsaron yankin, wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce bincikensu ya gano cewa, maharin ya tashi bom din da ke jikinsa ne a cikin masallacin lokacin da ake tsaka da sallah.
Wani ganau ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa ya ji karar fashewa har sau uku daga ainihin kofar shiga, inda mutane ke alwala.
Akalla motocin agaji 15 suka garzaya yankin da lamarin ya faru don gaggauta ceto rayukan wadanda suka jikkata.
Sai dai har kawo yanzu babu kungiyar da ta sanar da daukar nauyin kaddamar da wannan sabon hari.
Ko shakka babu IS na matsayin babbar barazana ga Taliban wadda ke gaba da kaddamar da makamantan hare-haren tun bayan da kungiyar ta kwace iko da Afghanistan a farkon watan Agusta.