Hukumomi a Somaliya sun tabbatar da mutuwar mutum shida bayan wani harin bam da aka kai a wajen wani masallacin Juma’a a birnin Kismayo.
Rahotanni kuma sun ce ana fargabar akalla wasu mutum 20 sun samu munanan raunuka a harin da ake zargin an kai shi ne kan wani fitaccen dan siyasar yankin.
“Wani dan kunar bakin wake da ya yi damara da abubuwan fashewa ya kai hari a masallacin Juma’a na Qaadim a tsakiyar birnin a daidai lokacin da mutane ke kokarin fita bayan kammala sallar Juma’a”, inji Abdinnasir Gulled.
Birnin Kismayo dai na da matukar muhimmanci a Somaliya kasancewar shi yake dauke da babbar tashar jiragen ruwa ta kasar.
Tuni dai kungiyar Al-Shabaab ta bakin gidan rediyonta na Andulus ta dauki alhakin kai harin.
Kungiyar wacce ke da alaka da ta Al-Ka’ida na yawan kai hare-hare a kan jami’an gwamnati, ’yan jarida, fitattun ’yan kasuwa da kuma sauran mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kasar mai fama da rikici.