✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hari kan Zulum: Gwamnoni za su yi zama da Buhari

Gwamnoni za su tattauna da Shugaba Buhari kan tabarbarewar yanayin tsaro a Najeriya

Kwamitin Tsaro na Majalisar Zartarwa ta Kasa, zai yi zama a ranar Talata kan harin da aka kai wa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum.

A ranar Laraba wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kai wa ayarin gwamnan hari a hanyarsa ta zuwa duba ‘yan gudun hijira.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Ekiti, John Kayode Fayemi, ya ce gwamnonin za su tattauna da Shugaba Muhammadu Buhari kan abun da suka kira “tabarbarewar yanayin tsaro”.

A wasikar da ya aika wa Zulum a ranar Litinin, Faymei ya ce Gwamnonin na tare da Zulum da jama’ar Jihar Borno sakamakon abun da ya faru, wanda suka ce babban ci baya ne a bangaren tsaron kasa.

Ya ce ‘ya’yan kungiyar suna kuma bayan Zulum dari bisa dari a kokarin kawar da “miyagun wakilan shaidan da ke aiwatar da barna”.

Ya kuma ce gwamnonin sun damu da lalacewar tsaro a kasa duk da kaimin da gwamnati ta saka na ganin ta magance matsalar.

Idan ba a manta ba, a ranar Lahadi Gwamna Zulum ya jaddada cewar akwai masu kokarin dakile yunkurin kawo karshen Boko Haram a Najeriya.

A lokacin da ya karbi bakoncin Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC da gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya jagoranta, ya yi kira ga Shugaban kasa da ya kara yi wa yanayin tsaron kasar kallo na basira.

Mai Magana da Yawun Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Kanar Sagir Musa, ya ce rundunar ta fara bincike a kan harin da aka kai wa gwamnan a ranar Laraba.