✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hare-haren Nasarawa da Zamfara sun lakume rayuka 30

Dalibai sun tsallake rijiya da baya a Zamfara inda mahara suka bindige mutum 13

Mahara sun yi wa mutum 17 kisan gilla ciki har da Dagacin unguwar Osewu, Abubakar Omazi a Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa.

Sun kuma bindige mutum 13 a Jihar Zamfara washegarin da Gwamnatin Tarayya ta ba su wa’adin wata biyu su mika wuya ko su dandana kudarsu.

A safiyar ranar Larabar ce ‘yan bindiga a Jihar Nasarawa suka kai wa yankin Osewu farmaki inda suka yi ta sarar mazauna da adduna.

Wani mazaunin garin mai suna Yahaya ya ce Mataimakin Shugaban ‘Yan Bangar unguwar na daga cikin wadanda aka kashe kuma wasu gawarwakin an gano su ne a cikin daji.

Aminiya ta gano cewa Shugaban Karamar Hukumar Toto, Nuhu Dauda da jami’an tsaro sun ziyarci yankin bayan harin domin jaje da kuma daukar matakai.

Sai dai kuma kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel ya ce ba su samu labarin ba tukuna.

An kashe mutum 13 a harin Zamfara

Da Azahar din ranar Larabar ce kuma ‘yan bindiga suka aika mutum 13 lahira a unguwar Dagama da ke Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Mazauna sun ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne a kan babura suna harbin mazauna.

“Sun shigo yankin da misalin karfe daya na rana sun harbin jama’a; Dalibai na daukar darasi a makarantar sakandaren unguwar, amma da ganin maharan sai suka ruga domin samun tsira.

“Yanzu hakak an gano gawarwakin wadanda aka kashe muna shirin yi musu jana’iza,” kamar yadda wani mazaunin garin, Musa Damaga, ya shaida wa Aminiya.

Mun tuntubi mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, amma ya ce: “Ku jira tukuna, zan kira ku daga baya.”

Harin na Zamfara na zuwa ne ‘yan sa’o’i bayan Gwamna Bello Matawalle ya sanar cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura karin sojoji 6,000 domin ragargazar ‘yan bindiga a Jihar.

Gwamnan ya yi bayanin ne bayan ganawa da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya wadanda suka ziyarci Jihar domin ganawa da shi da sarakuna da kwamandojin soji kan matsala tsaron da ke addabar Jihar.