Rundunar Sojin Najeriya za ta haska bidiyon hakikanin abin da ya faru a harbin da ake zargin jami’anta da yi lokacin zanga-zangar #EndSARS a Lekki.
Wakilan rundunar sun bayyana da faifen bidiyon ne a safiyar Asabar ranar da Kwamitin Shari’a mai binciken lamarin da Gwamnatin Jihar Legas ta kafa, zai ci gaba da zamannsa.
Sojojin da lauyansu A.B. Keyinde sun sha musanta zargin harbin masu zanga-zangar #EndSARS a daren ranar 20 ga Oktoba, 2020 a Lekki.
Sun kuma ce a shirye suke su haska bidiyon takamaimen abin da ya faru tsakanin jami’ansu da masu zanga-zangar a wurin.
Runduna ta 81 ta Sojin Kasa ta gabatar da sunayen Laftana Janar uku da Kanar daya da za su bayar da shaida a gaban kwamitin.
Harbin da ake ce-ce-ku-cen a kansa shi ne ake ganin ya kai ga kazancewa zanga-zangar a sassan Najeriya tare da haddasa asarar da ba a kai ga tantance iyakanta ba.
Kwamitin na Doris Okuwobi ya dage zamansa ne da sati biyu bayan wasu wakilan #EndSARS sun kaurace masa saboda Babban Bankin Najeriya (CBN) ya rufe asusun ajiyansu saboda daukar nauyin zanga-zangar.