✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harbin kunama

Wani Babarbare ne yana noma shi da karamin dansa sai kunama ta harbi yaron, ya fashe da kuka. Sai kawai ya yi ta marin yaron…

Wani Babarbare ne yana noma shi da karamin dansa sai kunama ta harbi yaron, ya fashe da kuka. Sai kawai ya yi ta marin yaron yana cewa: “Don dan wannan kwaron ya cije ka kake kuka?” Baban ya sa hannu ya kama kunamar zai jefar sai ta harbe shi, ya yi ta tsalle da ihu, yana cewa: “Buba ka yi kuka da kyau sosai, wannan kwaron mugu ne!” 

Daga Sani Babawuro Jama’are, 08093435003