✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Har yanzu NCC ba ta sabunta lasisin kamfanin MTN ba

Hukumar NCC ta karyata cewa ta sabunta lasisin MTN na karin shekara 10.

Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce har yanzu ba ta sabunta lasisin aikin kamfanin sandar na MTN a Najeriya ba.

NCC ta karyata labaran da ke yawo a intanet cewa hukumar ta sabunta lasisin kamfanin na MTN na tsawon shekara 10 masu zuwa.

Mai magana da yawun Hukumar, Ikechukwu Adinde, ya ce “NCC ta lura da wani labari a intanet mai taken “Gwamnati ta sabunta lasisin MTN bayan shekara 20 da fasa sadarwar GSM a Najeriya’ inda labarin ya nuna Hukumar ta sabunta lasisinsa na karin shekara 10”.

Ya bayyana cewa MTN dai ya mika bukatarsa na neman hukumar ta sabunta lasisinsa, amma hukumar ba ta amince ba tukuna.

A cewarsa, Hukumar na kan aikin duba takardun domin tabbatar da kamfanin ya cika sharuddan da suka kamata, kafin a kai ga matakin amincewa ko kin sabunta lasisin kamfanin.