Har yanzu Babban Bankin Najeriya (CBN) bai ba wa bankunan kasuwanci tsoffin takardun kudi da za su ba wa kwastomominsu ba, duk da cewa ya umarce su da su ci gaba da bayarwa da kuma karbar tsoffin takardun N1,000 da N500 da kuma N200 da ya sauya wa fasali.
Duk da umarnin CBN na ci gaba da amfani da tsofifn takardun kudin, ’yan tireda, masu sana’ar hannu, dalibai, masu harkar hada-hadar kudi na POS da suka je cirar kudi a bankuna a Abuja, sun koka cewa sun kasa samun adadin kudin da suke bukata.
Sun bayyana wa Aminiya cewa wadansu daga cikinsu sun samu N5,000 wasu N10,000 wasu kuma N20,000.
A ranar Litinin ne da CBN ta hannun kakakinsa, Isa AbdulMumin, ya umraci bankunan kasuwanci su ci gaba da amfani da tsoffin kudaden da aka sauya wa fasali, har zuwa ranar 31 ga watan Disamba, 2023.
Sanarwar ta fito ne sa’o’i kadan bayan Fadar Shugaban Kasa ta nesanta Shugaba Buhari daga CBN da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami da suka ki bin umarnin Kotun Koli na ranar 3 ga watan Maris, kan ci gaba amfani da tsoffin kudin.
Sai dai zuwa ranar Talata, CBN bai ba wa bankunan tsoffafin kudaden da suka kai masa ba, domin ci gaba da harkokinsu, duk da cewa wasu bankunan sun ci gaba da bai wa kwastomomi tsoffin kudaden da ke hannunsu.
Hakan kuwa na faruwa ne a yayin da jama’a suka yi dafifi a rassan bankunan domin samun kudaden, bayan samun labarain umarnin babban bankin.
‘Kudin wurinmu CBN ya ce mu bayar’
Wani jami’i a bankin Polaris ya shaida mana cewa, “Ba mu karbi kudi daga CBN ba saboda har yanzu muna da tsoffin.
“Umarnin CBN shi ne cewa mu bayar da tsoffin kudaden da ke hannunmu; nan gaba idan suka kare za mu samu umarni game da mataki na gaba da za a dauka.”
Shi kuma wani babban jami’i a bankin GT ya shaida mana cewa, “Ba mu karbi tsoffin kudi daga CBN ba, amma muna da tsoffin kudi da za su wadace mu, kuma su muke ba wa kwastomominmu a yau.”
Ya bayyana cewa bankuna sun rike tsoffin kudaden da ke hannunsu tun kafin ranar 10 ga watan Fabrairu, gabanin umarnin CBN na farko da ya kara wa’adin amfanin da kudaden.
Ya ce, “Da ma kudaden suna hannunmu; lokacin da abin ya sha kan CBN bayan mutane suna ta tururuwar kai masa tsoffin kudaden, sai ya ce su kawo mana, waddannan kudaden su ma suna nan mun ajiye.”
Bankuna sun bi umarnin CBN
Tuni dai bankuna suka bi umarnin CBN na amfani da tsoffin kudaden kamar yadda Aminiya ta gani a rassan bankunan Sterling, GTB, First Bank, UBA, da kuma Access Bank a Jihar Kano.
Wata mai hulda da banki, Misis Gabriel, ta shaida mana cewa, “Yau bankina ya ba ni N20,000 na tsoffin N500. Na ji dadi saboda ta yi makonni rabona da rike tsabar kudi kamarsu.”
A sassan Jihar Legas kuma injinan ATM na ba da kudade a wurare da dama, kuma an samu raguwar cunkoson mutane a bankuna idan aka kwatanta da kwanakin baya.
A reshen bankin Polaris da ke Iju, ana ab wa kowane kwastoman banki N10, 000 sabanin N20,000 da CBN ya kayyade.
A bankin UBA da ke yankin Bwari da ke Abuja, ana iya cirar N5,000 a reshen bankin na da kuma Yankin Kasuwanci kuma ana cirar N10,000.
Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na Bankin Unity, Matthew Obiazikwor, ya shaida mana cewa bankin ya bi umarnin CBN 100%.
“Muna ba wa kwastomomi kudi kuma muna bin umarnin CBN dari bisa dari. Mun loda kudi a ATM dinmu, sai dai an riga an kayyade abin da mutum zai iya cira a kowace rana,” in ji shi.
’Yan kasuwa sun yi turjiya
Sai dai duk da haka ’yan Najeriya na kokawa cewa wasu ’yan kasuwa na kin karbar tsoffink kudaden, duk da umarnin na CBN.
Wasu direbobin motocin haya sun ki karbar tsoffin N500 da N1,000 a yayin da a Jihr Kaduna, ’yan kasuwa ke dar-dar wajen karbar kudaden, saboda tsoron baya za ta iya haihuwa.
Wani mai sayar da doya, Muhammad Isah, ya ce, “Ba zan karba ba, sai na ji Shugaba Buhari ya ce a fara karba.”
Aminiya ta gano cewa shugabannin kasuwanni a Jihar Legas sun fara wayar da kan ’yan kasuwa cewa su ci gaba da karbar tsoffin takardun kudin bisa umarnin CBN.
Iyaloja ta Kasuwar Asejere da ke Makoko, Alhaja Kasarat Adebayo, ta ce, “Na sanar da mutanena, gobe ma zan kara sanar da su. Mun ce musu su rika karbar tsoffin kudaden daga hannun kwastomomi.”
Gwamnatocin jihohi sun yi kira a karbi tsoffin kudade
Gwamnatin jihohin Kano, Jigawa, Delta, Ogun, Kogi, Legas na daga cikin wadanda ke ta kiraye-kiraye ga jama’arsu cewa su ci gaba da amfani da tsoffin kudin har zuwa ranar 31 ga watan Disamba.
A nasu bangaren, kwararru, sun bukaci CBN ya fito da tsoffin takardun kudin da ke hannunsa a ci gaba da amfani da su, zuwa lokacin da wa’adin amfanin nasu zai kare.
Idan ba a manta ba, CBN ya sanar cewa kafin fara aikin Dokar Takaita Amfani da Tsabar Kudi, akwai Naira tiriliyan 3.2 da ke yawo a hannun jama’a, amma ta yi nasarar dawo da tiriliyan N2.3 hannunta da kuma bankunan kasuwanci.
Wani mai sharhi kar harkar hada-hadar kudade, Farfesa Uche Uwaleke, ya ce umarnin Kotun Koli ba shi da wani amfani muddin ba a dawo da tsoffin kudin an ci gaba da amfani da su ba.
Ya ce, “Damuwata ita ce, idan ba dawo da tsoffin kudaden kuma a jingine dokar kayyade cirar tsabar kudi ba, karancin kudin ba zai kau ba.”
Ya kara da cewa, “Aminicewar CBN ya ci gaba da amfani da tsoffin kudaden abu ne daban, wadatar da jama’a da kudaden kuma wani abu ne daban.”
Shi kuma wani kwararre kan harkokin cigaba, Joseph Momoh, cewa ya yi: “Duk da cewa bankuna sun bi umarnin CBN, amma abin da suke bayarwa ba zai wadatar ba.
“Ya kamata babban bankin ya fito da tsoffin kudaden da ya tara a ci gaba da amfani da su,” in ji shi.
Shi kuma wani kwararren akanta, Umar Mohammed, wanda ke ba da shawara ga wasu bankuna, ya bayyana cewa dole sai bankuna sun yi ta maza kafin su iya magance matsalar karancin kudi.
“Ba wanda ke cewa CBN ya dawo da tiriliyan N2.3 ta aka mayar masa. Amma a bayyana yake cewa Najeriya ba ta kai matakin amfani da irin wannan tsari ba.
“Abin da ya faru ya nuna karara cewa bankuna ba su da karfin da ake bukata, sannan akwai miliyoyin ’yan Najeriya da ba sa ajiya a bani. Bugu da kari akwai bukatar a kara wayar da kan al’umma.
“Don haka ina kira ga CBN ya daure ya karbi wannan gaskiyar. Sannan akwai mutanen da suka rungumi wannan tsari na CBN, kuma wannan abin a yaba wa CBN din ne,” in ji shi.
Daga Sagir Kano Slaeh, Sunday M. Ogwu & Philip S. Clement (Abuja), Abiodun Alade (Legas), Maryam Ahmadu-Suka (Kaduna) & Meluwa Kelvin (Asaba)