✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Har yanzu ban yanke shawarar fitowa takara ba —Gwamnan CBN

Ina mika godiya ta musamman ga wadanda suka sayi tikitin takarar shugaban kasa a madadi na.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele, ya ce har yanzu bai yanke shawarar fitowa takarar shugaban kasa ba a Zaben 2023 da ke tafe.

Cikin wasu jerin sakonni da Mista Emefiele ya wallafa ranar Asabar a shafinsa na Twitter, ya ce a yanzu abin da ya sa gaba shi ne ci gaba da sauke nauyin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta rataya masa.

Emefiele mai shekara 60 na mayar da martani ne bayan rahotannin da suka karade kafofin yada labarai a ciki da wajen Najeriyar cewa ya sayi fom din takarar ranar Juma’a.

Sai dai duk da haka Gwamnan Babban Bankin bai yi watsi da maganar fitowarsa takara ba, inda ya ce nan da ’yan kwanaki zai yanke shawara.

Aminiya ta ruwaito Gwamnan Babban Bankin kasar yana yi wa wadanda suka saya masa tikitin takarar, sai dai ya ce idan ya yanke shawarar fitowa takara zai yi amfanin da kudinsa wajen sayen tikitin ba sai wasu sun saya masa ba.

“Na ji dadi da aka samu wasu manoma da masu kishin kasa suka hada gudunmuwar kudi suka saya min fom din takarar kujerar shugaban kasa na jami’yyar APC, sai dai har yanzu ban yanke shawara a kan hakan ba, amma ina mika godiya ta musamman a gare su.

“Ina godiya da sha’awar da wasu kungiyoyi ke nunawa gare ni don na fito takarar shugaban kasa…wannan babban mataki ne da ke bukatar taimakon Allah: nan da ’yan kwanaki kuma Allah zai yi min jagora.

“Idan har ta kasance zan amsa kiran masu son na tsaya takara, to zan yi amfani da gumina da kuma karfin aljihuna a kudaden da na samu a aikin banki wanda na shafe shekaru fiye da 35 ina yi wajen sayen fom din takarar da kaina.”

A bayan nan dai ana ci gaba da yi wa Mista Emefiele matsin lamba tun bayan da ta bayyana cewa ya yanki tikitin ayyana neman takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar APC a ranar Juma’ar da ta gabata.

Daga cikin wadanda suka fusata da bullar rahoton har da Gwamnan Jihar Ondo, Mista Rotimi Akererdolu da ya nemi Shugaba Buhari ya gaggauta tsige Gwamnan Babban Bankin kasar.

Akeredolu ya shawarci Shugaba Buhari da ya tsige Mista Emefiele, don idan ba haka ba kwamacalar da ake yi a harkar siyasa da gwamnatin kasar za ta wuce gona da iri.