✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu ban kalli yadda Manchester United ke taka leda a karkashin Mourinho ba – Pep Guardiola

Sabon kocin kulob din Manchester City na Ingila, Pep Guardiola ya ce har yanzu bai kalli yadda kulob din Manchester United ke yin kwallo a…

Sabon kocin kulob din Manchester City na Ingila, Pep Guardiola ya ce har yanzu bai kalli yadda kulob din Manchester United ke yin kwallo a karkashin sabon kocinsu Jose Mourinho ba.
Kawo yanzu an buga wasanni uku a gasar kenan inda kulobh din Manchester City ke gaba sai kulob din Chelsea a matsayi na biyu yayin daManchester United ke matsayi na uku. Dukkan kungiyoyin sun samu nasara a wasanni uku-uku da suka yi, abin da ya bambanta su kawai shi ne yawan kwallaye da suka zura a raga.
A ranar 10 ga wannan wata  ne za a kece raini a tsakanin Manchester United da kuma Manchester City a filin wasa na Old Trafford.
Pep Guardiola wanda ya sha haduwa da Jose Mourinho a lokuta daban-daban a lokacin da suke aikin horarwa a Sifen ya nuna ba ya shakkar haduwa da kulob din Manchester United da ke karkashin Mourinho a wannan lokaci.  Hasalima ya sha alwashin yin biji-biji da United a gaban magoya bayansu da hakan zai ba kulob din City dama cigaba da rike ragamar gasar ta firimiya.  Kocin ya ce yana fata zaratan ’yan kwallonsa ba za su samu rauni kafin wasan ba.
Pep Guardilola ne ya kafa tarihin kocin da ya taba lashe wa kulob din FC Barcelona na Sifen kofuna shida a kakar wasa daya.
Daga baya ne ya canza sheka zuwa kulob din Bayern Munich da ke Jamus sannan a bana ya koma Ingila inda ya cigaba da aikin horarwa a kulob din Manchester City.