Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ce har yanzu cutar coronavirus tana nan ba ta gushe ba.
Gwamnan ya fadi haka ne a Lafiya, inda ya jaddada muhimmancin gargadin jama’a su guji karya dokar kariya daga cutar.
- Mutanen da cutar Coronavirus ta harba a Najeriya sun zarta dubu 58
- ‘Kashi 20 na mutanen Afirka ta Kudu suna dauke da Coronavirus’
A cewarsa, “Duk da cewa jihar ta samu nasarar hana yaduwar cutar, har yanzu cutar na nan.
“Don haka ya dace jama’a su rika kiyaye sharuddan da aka hukunta don kare kai”.
Gwamnan ya ce an yi wa mutum 3,751 gwajin cutar ana kuma jiran sakamakkon gwajin mutum 15.
Mutum 449 ne suka kamu da cutar, an sallami 346, ana jinyar 88 a gidajensu wasu 13 kuma sun rasu.
Gwamnan ya yaba wa Kwamitin Yaki da cutar na Jihar, karkashin Mataimakinsa, Dokta Emmanuel Akabe.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta hannun Kwamitin Shugaban Kasa ta ba jihar gudunmawar Naira biliyan daya don yaki da cutar.