Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ce fiye da Naira biliyan 500 na tsofaffin takardun kudi ne har yanzu ke hannun ’yan siyasa ba a mayar bankuna ba.
Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana hakan a wata tattaunawarsa da gidan Talabijin na Channles, ranar Alhamis.
Ya ce, “A ganinsu mafitar da suke da ita kawai shi ne su sayi kuri’un mutane, saboda na’urar BVAS za ta bayar da mamaki kwarai a wannan karon.
“Wasu daga cikinsu sun boye kudi musamman saboda haka, don haka har zuwa wannan lokacin akwai fiye da biliyan 500 na tsoffin kudin da ba a mayar wa CBN ba.
“Muna da hanyoyin bankado wadannan bayanan sirrin, kuma za mu yi amfani da su fiye da kowanne lokaci,” in ji Abdulrashid.
Tuni dai wa’adin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar na daina amfani da takardun kudi na N1,000 da N500 da kuma N200 ya cika.
Sai dai a wani jawabi da ya gudanar a makon da ya gabata, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin ci gaba da amfani tsofaffin takardun N200 har nan da ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa.