✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu akwai layukan waya miliyan 29 da ba a hada da lambar NIN ba

NCC dai a baya ta lashi takobin rufe layukan da suka gaza yin hakan bayan cikar wa'adin.

Yayin da wa’adin farko da Gwamnatin Tarayya ta bayar yake cika akan hada layukan waya da Lambar Shaidar Zama dan Kasa (NIN) a ranar Talata, akalla layuka miliyan 29 ne har yanzu ba su kai ga yin hakan ba.

Wata majiya a Gwamnatin Tarayya ta tabbatarwa da Aminiya cewa ya zuwa ranar Litinin, akwai kusan layuka miliyan 176 da aka riga aka hada su da lambar.

Tun da farko dai gwamnatin ta bayar wa’adin ranakun 19 ga watan Janairu da kuma tara ga watan Fabrairun 2021 ga dukkan masu lambar zama dan kasan da ma wadanda basu da ita da su hanzarta yin hakan kafin wa’adin domin kaucewa rufe musu layukan.

To sai dai kakakin Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami, Uwa Sulaiman ba ta amsa bukatar wakilin mu ba ta neman sanin makomar wadanda suka yi kunnen kashi da wannan umarnin bayan cikar wa’adin.

A baya dai Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) dai ta lashi takobin rufe dukkan layukan da suka gaza yin hakan da zarar wa’adin ya cika.

“Wani bincike da muka yi a kwanan nan ya nuna cewa akalla kusan kowanne dan Najeriya na da layuka hudu zuwa biyar. Wannan ne dalilin da ya sa muka ce za mu kyale mutum daya ya hada lambobinsa har guda bakwai da lambar NIN daya,” inji NCC cikin wata sanarwa da ta fitar a kwanan nan.