✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Har ’yan kwalejin ilimin kimiyya da fasaha nake koya wa kere-kere’

Malam Garba Lawan matashi ne mai sanaár walda da kira a Gombe, wanda kuma ya kware wajen kere-kere. Ya kera wata keke mai kafa uku,…

Malam Garba Lawan matashi ne mai sanaár walda da kira a Gombe, wanda kuma ya kware wajen kere-kere. Ya kera wata keke mai kafa uku, wato Keke-Napep, a karon farko, wadda wasu mutane suka saya suka tafi da ita Maiduguri. Sannan ya sake kera wata, wacce ta sha bamban da ta farko, wadda ganin haka ya sa Kwalejin Ilimin Fasaha ta Tarayya (FCE Technical) da ke Gombe ta dauke shi don koya wa dalibanta yadda ake wannan kira. Aminiya ta sami zantawa da shi kan wannan sana’a ta kere-kere, kamar haka:
Aminiya: Me ya ba ka shaáwa har ka kera Keke-Napep?
Garba Lawan: Shaáwar ce kawai, domin ni walda nake yi. Sannan kuma ganin yadda ake shigo da kekunan daga kashashen waje ga kuma wasu jihohi a nan Arewa an fara hana hawa Babura, wanda hakan zai sa masu sanaár kanikanci fadawa wata rayuwa ta rashin abin yi.
Aminiya: Wannan keke ita ce ta nawa da ka kera?
Garba Lawan: Ta biyu ce. Ta farkon ba ta kai wannan ba, wadda dayake a kan ta na fara, na samu matsaloli, amma a wannan ba matsala sosai. Ta farkon kuma wasu ’yan Maiduguri ne suka saya suka tafi da ita can.
Aminiya:  Ya aka yi kwalejin ilimin kimiya da fasaha ta gwamnatin tarayya ta dauke ka kana koya wa dalibanta yadda kake kera wannan keke?
Garba Lawan: Alhamdulillah, a hira da ka yi da ni a jaridar Aminiya, lokacin da na kera ta farko, malaman suka ga hotona da keke-napep din, dayake da ma su ma suna da shaáwar kera keke-napep din shi ne suka neme ni.
Aminiya: Da suka dauke ka kana koyawa daliban, akwai abin da suke biyanka ne?
Garba Lawan: Eh, suna ba ni dan wani ihisani wanda bai taka kara ya karya ba, kuma ni ma a hakan ina sake karuwa da su ta wani bangare. Sai dai su ba irin wacce na kera muke yi da su ba, wata daban ce, wacce ita gaban inda mai tukawa yake a rufe yake sannan bayan yana da bodi rabi a bude.
Aminiya: Ganin ka iya wannan sanaá, wane kira kake da shi ga gwamnati ko masu hannu da shuni na ganin sun taimaka maka?
Garba Lawan: Kirana shi ne gwamnati ta shigo ta taimaka min da kayan aiki irin na zamani da kudi wanda zan dinga sayen kayan aiki, ina ci gaba da kera wasu irin kayayyakin daban.
Aminiya: Kana ganin idan gwamnatin ta taimaka maka me za ka iya kerawa nan gaba, idan ka samu kayan aikin da kake magana?
Garba Lawan: Sai dai an samu din, domin ina da burin yin kere-kere da daban-daban masu amfani, wanda ba sai na sayi na kasashen waje ba.
Aminya: Daga karshe wane kira kake da shi ga matasa.
Garba Lawan: Eh, kira a nan shi ne su kasance masu kishin neman na kansu da rungumar sanaá komai kankantar ta, saboda akwai rufin asiri mai yawa a harkar sanaár hannu.