✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin inganta al’umma ta fannin Kimiyya da kere-kere (3)

A nan ba ina wanke Turawa ba ne cewa ba su yin sihiri, ko kadan.  Suna yi. Ba ma su kadai ba, kowace al’umma tana…

A nan ba ina wanke Turawa ba ne cewa ba su yin sihiri, ko kadan.  Suna yi. Ba ma su kadai ba, kowace al’umma tana da irin gargajiyarta, wanda a ciki ba a rasa wani nau’i na surkulle ko sihiri.  Amma a wannan bangare babu wani abu wai shi sihiri.  Ilimi ne kawai tsantsa.  Abin da ke tabbatar mana da hakan kuwa shi ne, akwai da yawa daga cikin bakaken fata da suka koyo wannan nau’in ilimi.  Da akwai wani nau’i na sihiri a ciki da tuni sun sani.  Kuma da sun yada shi ga al’umma, ko dai don a kauce masa, ko kuma don abin da suka koyo ke nan.
Wani abin mamaki ma shi ne, galibin wadannan na’urori da ake kerawa musamman a fagen sadarwa, duk za ka samu asalin wadanda ke aiki a kansu ba turawa bane, bakaken fata ne.  Idan ka je kamfanin Apple, da kamfanin Microsoft, da kamfanonin kera motoci irin su Honda, da Toyota, da Ford Motors, duk za ka samu galibi bakaken fata ne.  Cikin shekarar da ta gabata tashar talabijin CNN ta yi hira da wani matashi dan Najeriya, haifaffen Jihar Sakkwato, wanda ke aiki a kamfanin BMW da ke kasar Jamus.  Daidai lokacin kamfanin ya fitar da wata nau’in mota kirar BMW wacce kowa ke yabawa.  Da bincike ya yi nisa, sai aka gano ashe wannan matashi mai suna Zailani Aliyu ne ya zana asalin kwarangwal din motar gaba dayanta.  Haka ma sashen Hausa na BBC ya taba hira da wani bawan Allah da ke aiki a wani kamfanin kera motoci da ke kasar Jamus, wanda Injiniya ne, masanin makaman kera motocin zamani. Bahaushe ne dan Najeriya.  Ire-iren wadannan mutane suna da yawa, ba a jin ko duriyarsu, saboda dadewarsu a kasashen waje, musamman sanadiyyar yadda tsarin mulki da shugabanci ya tabarbare a kasarmu.
Mu dawo kan zancenmu na sihiri.  Ba abin da ke taimakawa wajen samuwar ire-iren wadannan na’urori sai tsantsar ilimi, da kuma kwazo da himma dawwamammu.  Wadannan su ne tafarkin tsira.  Shi ilimi muddin ka rike shi da mahimmanci, ka bashi hakkinsa, ka ririta shi ta hanyar dabbaka abin da ka koya, zai samar maka da hanyoyin sauki a rayuwarka, ya zama sanadiyyar inganci da habbaka ga al’ummar da kake rayuwa a cikinta.  Wannan shi ne abin da ke faruwa.  Ba wai cewa Turawa sun fi mu gaskiya ba ne dari bisa dari, ba wai sun fi mu kwakwalwa ba ne, ba wai sun fi mu iya sauraron malami ba ne a cikin aji, ba wai sun fi mu imani ba ne da Allah, illa sun baiwa ilimi muhimmanci ne, sun ririta shi, sannan suka juya shi ta yadda suke so.  Shi yasa duk da maguzancinsu, idan kaje kasashensu za ka ga bayyanannen ci gaba ta fannin gine-gine, da zane-zane, da kere-kere da kuma ingancin lafiya a rayuwarsu.  Duk wannan ba wani abu ba ne ya taimaka musu illa rikon ilmi da suka yi da mahimmanci.
Mafita
A karshe zan yi kira ga matasa musamman, domin su ne masu jini a jika, da su riki ilmi da muhimmanci. Wajibi ne ga duk mai son ci gaba a fannin ilmi musamman na kimiyya da kere-kere, ya lazimci abubuwa kamar haka:
Hakuri da Juriya:  Wadannan dabi’u guda biyu suna da mahimmanci wajen ci gaban rayuwa baki dayansa; daga rayuwar addini zuwa fannin mu’amala.  Hujja kan haka kuwa ba sai na kawo mana nassoshin shari’a ba, hatta a al’adance mun san wannan.  Har wa yau duk wanda ka ga ya zama wani a duniya, har ana yi da shi a fannin da ya shahara, idan ya baka labarinsa za ka ga sai ya lazimci hakuri da juriya. To haka karatu yake, musamman fannin da mutum ke son kwarewa a kai, dole sai ya lazimci hakuri da juriya.  Hakuri shi ne danne zuciya wajen daukan abin da al’adance ba za ta iya ba, ko barin abin da a al’adance ba za ta so bari ba.  Shi kuma juriya shi ne tabbata kan hakuri na tsawon lokaci.  Idan hakuri bai samu ba, to, juriya ba ya samuwa.  Sai an jure.
Kyakkyawar Niyya:  Wannan shi ne manufa kan abin da kake son kaiwa gare shi.  Wasu kan dage ne su jure don suna son sunansu ya shahara a duniya.  Wasu kuma don al’umma su amfana da kokarinsu.  Su kuma wasu don su samu abin duniya, ko abin hannu.  Manufarka ce za ta taimaka maka wajen daukan kowace irin dawainiya – na kashe lokaci ne, ko wahala, ko ciyar da dukiya –  don ganin ka cinma burinka.  Amma muddin ba ka da manufa cikin abin da kake yi, zai yi wahala ka iya jure dawainiya da wahalar da ke dauke cikin yin abin ko nemansa, a al’adance.  Amma idan kana da manufa, duk irin wahalar da za ka sha, da zarar ka yi niyyar fasawa ko hakura da abin, sai zuciyarka ta tuna maka cewa ga fa dalilin da yasa kake neman wannan abu, nan take sai kaji ka kara samun kaimi.
Hanyoyin Kariya:  Bayan hakuri da juriya da kyakkyawar manufa, idan fannin da kake karantawa ko kokarin nakaltarsa fanni ne mai dauke da hadari ga rayuwa ko lafiyarka, dole ne ka nemi hanyoyin kariya, don rayuwa ta kara inganci.  Kuma ma zai yi wahala ka samu wani fanni na ilimi mai dauke da hadari wajen koyo amma babu hanyoyin kariya ga masu koyonsa ko masu dabbaka shi bayan sun koya.  A takaice dai, kada samuwar hadari cikin fannin karatu ya hana ka koyon wannan fanni, musamman idan kana da sha’awa kansa.  Domin, kamar yadda bayani ya gabata ne a baya, babu wani abu a rayuwa wanda ba ya dauke da hadari a cikinsa, hatta cin abinci, da shan duk wani abin sha, da lasar duk wani abin lasawa, za ka samu akwai hadari a cikinsa.   Abin da kawai za ka duba shi ne maslahar da ke ciki, ma’ana tarin fa’ida da za ka samar wa al’umma bayan ka kware a wannan fanni.
Bukatun Al’umma:  Da yawa daga cikin magabata wadanda suka yi wa al’umma hidima a fagen ilimi sun yi haka ne ta la’akari da abin da al’ummar da suke ciki take da matukar bukatuwa zuwa gare shi.  Wannan ma shi ne babbar makasudi da ake so duk wani mai bincike a fagen ilmi musamman na kimiyya ya rika la’akari da shi a duk sadda ya zo gudanar da wani bincike.  Wannan ne zai sa a samu fa’ida cikin abin da aka gabatar, babu maimaici mara fa’ida.  A matsayinka na dalibi mai niyyar shiga jami’a, idan ba ka da wata bukata ta kashin kanka kan fagen da kake son karantawa, to ka dubi meye al’umma ke da bukatuwa zuwa gare.  Wannan zai baka gamsuwa, da kuma ambato na gari a baki jama’a, bayan lada da za ka samu.

Kammalawa
A kowane irin al’amari na rayuwa dole ne a samu kalubale.  Wannan al’adar rayuwa ce.  A matsayinka na dalibin ilmi matashi, wajibi ne ka nemi hanyoyin fuskantar wadannan kalubale, tare da kokarin cin nasara a kansu.  Babu wata al’umma da taba ci gaba ba tare da sadaukar da kai ba.  Shi kuma sadaukar da kai ba abu ne da ke kan hukuma kadai ba, a a, daga kan daidaikun mutane yake farawa, har a wayi gari tsarin ya zama na hukuma.  Domin ba kowa ba ne hukuma face mutane.  Daga cikin hanyoyin da ke taimakawa mutum ya zama mai sadaukar da kai kuwa akwai hakuri da juriya, da kuma samun manufa ingatacciya wacce a kullum za ta rika tsinkayin matashi don kaiwa ga manufarsa a aikace.