Gwamnatin Tarayya ta ce aikin hanyoyi 711 da take aiwatarwa a fadin Najeriya ya sa ’yan kwangila na bin ta bashin biliyan N392.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana haka yayin amsa tambayoyi a kan kasafin Ma’aikatarsa na 2021 a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa.
- An ware wa gyaran hanyar Kano-Maiduguri karin N8bn
- Yadda aikin hanyar Abuja zuwa Kano ke jefa matafiya cikin kunci da hadari
Ya ce bashin na biliyan N392 ya zarce kudin da aka ware wa ma’aikatarsa a shekarar 2021.
A cewarsa hakan ta sa aka dakatar da kirkirar sabbin ayyuka domin samun damar kammala wadanda aka fara.
Ministan ya ce ma’aikatar na bukatar akalla Tiriliyan N6.62 domin aiwatar da ayyuka 711 a fadin kasar nan.
Ya kuma shaida wa kwamitin cewa hakan ce ta tilasta wa ma’aikatar zabar ayyukan mafiya muhimmanci tana aiwatarwa.
Shugaban kwamitin, Sanata Adamu Aleiro ya shawarci Fashola ya yi amfani da Kudaden Hukumar kula da Fansho don aiwatar da hanyoyin, amma ministan ya ce ba shi da hurumin yin haka.