✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyar magance warin jiki

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon mun kawo muku hanyar da za ku…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon mun kawo muku hanyar da za ku magance warin jiki.

Allah Ya halicci mutum da wasu kwayoyin halitta da suke tsartar da wani ruwan sinadari mai fitowa daga kofofin gashi da ake kira pheromones. Wannan sinadarin PHEROMONES yana kara janyo kusantar juna tsakanin miji da mata, ko mace da namiji ne, kamar irin yadda warin bunsuru da akuya ke kara janyo junansu musamman lokacin barbara. Amma a bangaren mutum, idan wannan pheromones ya yi yawa, yana haifar da warin jiki ko warin hamatta ta yadda za a rika kyamar mutum.
Su masu wannan halitta, ba za su ji warin sosai ba, saboda sun saba, amma abokansu za su rika ji. Saboda haka, duk wadanda suke da irin wannan sinadarin pheromones mai yawa, ya kamata su fahimci matsalar da suke fama da ita.
Hanyar magance warin jiki:
Masu warin jiki ana so su rika wanka akalla sau biyu a rana, bayan sun yi wanka sai su dangwali sinadarin Apple Cider binegar da auduga, sannan su goga a hammatarsu, ko kuma a matse lemon tsami, sai su goga ruwansa a hammata, sannan su bari ya bushe, kada a sa turare.
Masu warin hammata za su iya shafa man zaitun duk lokacin da suka yi wanka. Hakan zai taimaka wajen magance matsalar warin jiki.