Kwamitin Kula da Ayyuka a Majalisar Wakilai ya yi tir da tafiyar hawaniyar da aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna ya ke yi ba.
Shugaban kwamitin, Abubakar Kabir Abubakar ya nuna bacin rai cewa bayan wata 27 da fara aikin, dan kwangilar – Julius Barger – ya kasa kammala kashi goma cikin dari na aikin.
Ya ce Majalisar ba zai yarda da kara ko sisi ko lokacin kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna ba.
Abubakar ya koka kwarai cewar mutane da dama sun rasa rayukansu a hanyar sakamakon rashin kammala aikin da kuma rashin daukar matakan kariya daga hatsari ga masu bin hanyar.
A wata hira da’yan jarida a kan yanayin aikin, Abubakar ya ce jazaman ne dan kwangilar ya kammala aikin watan Mayu, 2021 kamar yadda ya yi alkawari.
Ya ce muddin Julius Berger ya kasa kammala aikin cikin wata taran da suka rage, to Majalisa za ta raba wa wasu kamfanonin aikin su kammala kafin karshen Mulki Buhari.
Abubakar ya ce saura wata tara lokacin da kamfanin ya diba ya kare amma bubu alamun za ya iya kammala shsi kamar yadda ya yi alkawari.