Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku ‘labarin hankaka mai wayo’. Labarin ya yi nuni ga illar yaudara. A sha karatu lafiya.
Taku, Amina Abdullahi.
A shekaru aru aru da suka wuce a wani dajin dabbobi, an yi wani hankaka mai wayo amma irin na kauye. Dabbobin sun yanke shawarar yakamata su zabi sarki a dajin domin sanya doka. Su dabbobin wadanda suka kunshi dila da zaki da giwa da sauransu sun yake shawarar sanya Zaki sarkin garinsu.
A bangaren tsuntsaye kuma sun yanke shawarar sanya hankaka ya shugabance su. Hankaka yana son ya zama sarki sai ya je gefen su zaki ya ce shi yana tare da su. Sannan ya sake komawa gefen tsuntsaye ya ce shi ma tsuntsu ne yana tare da su.
Dabbobin dai suna iya kokarinsu domin samo musu sarki sai suka samu labarin abin da hankakan yake yi. Sai suka yanke shawarar zaki ne zai zama sarki.
Su zaki suka ce da shi shi ba irin su ba ne sai dai ya je gefen tsuntsaye tun da yana da fukafuki. Da ya je wajen tsuntsaye sai suka ce ai hankaka yana haihuwa ne kai tsaye ba tare da ya saka kwai ba, don haka shi ba tsuntsu ba ne nan suka kore shi.
Hakan ta jefa hankaka a cikin matsala, shi ba ya bangaren dabbobi sannan kuma ba ya bangaren tsuntsaye. Shi ya sa ba a cika ganin hankaka yana yawo da rana ba sai da dare a lokacin da sauran dabbobi ke barci shi kuma a lokaci ne yake fita yawon neman abinci.
Manyan gobe ku kasance masu gaskiya da kuma rikon amana.