✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hanifa: Abdulmalik Tanko ya sake musanta laifin kashe dalibarsa

Abdulmalik ya sake musanta laifin kashe dalibarsa, Hanifa a gaban kotu.

Abdulmalik Tanko, wanda ake tuhuma da kisan dalibarsa Hanifa Abubakar mai shekara biyar a duniya, ya sake musanta zargin da ake masa a gaban kotu.

Wannan na zuwa ne a ranar Litinin yayin da kotun da ke zamanta a sakatariyar Audu Bako da ke Jihar Kano ta ci gaba sauraron shari’ar da ake yi, wanda alkali Usman Na’abba ke jagoranta.

Abdulmalik, wanda a baya ya amsa duk laifin da ake zarginsa da aikatwa, ya musanta uku daga cikin laifukan da ake tuhumarsa da su da suka hada da garkuwa, azabtarwa da kuma kisan karamar yarinyar.

Sai dai a yayi zaman kotun na ranar Litinin, ya yi amai ya lashe kayansa,  yana mai cewa laifin da ya aikata kadai shi ne ya yi garkuwa da yarinyar sannan ya bukaci kudin fansa na Naira 100,000.

Ya amsa cewar ya sace Hanifa ya kai ta makarantarsa ya rufe ta, sai dai ya ce ba shi da tabbacin ko shi kadai ne mutumin da ya ganta bayan rufe ta da ya yi.

“Ba ni da tabbacin ko ni ne mutum na karshe da na ganta, saboda na yi magana da wani game da ita. Amma ban kashe ta ba kuma ban ba ta guba ba. Na barta tana bacci amma ina dawowa sai na tarar da ita ta mutu.

“Da ni da mutum na biyu da na uku ba mu san yadda aka yi ta mutu ba.”

Aminiya ta rawaito yadda aka sace Hanifa Abubakar a ranar 4 ga watan Disamba 2021, a kan hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya, wanda daga bisani aka gano malamin makarantarsu, Abdulmalik Tanko ne ya kashe ta bayan ya bukatar kudin fansa miliyan shida a hannun iyayenta a Jihar Kano.

Da farko Abdulmalik Tanko ya amsa laifin sace Hanifa tare da kashe ta, ta hanyar ba ta guba, sannan ya tona rami ya birne ta a cikin makarantarsu.

Tuni dai Abdulmalik da wadanda suka taimaka masa; Hashim Isyaku da Fatima Bashir sun shiga hannun jami’an tsaro, wanda daga bisani aka gurfanar da su gaban kotu, inda ake tuhumarsu da aikata laifuka biyar, wanda suka saba da sashe na 97, 274, 277 da 221 na kundin laifuka na ‘penal code’.

A wannan karo an sake dage shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Mayu don ci gaba da zaman kotun.