✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hana ’yan bindiga sakat nake so ku yi —Buhari ga Hafsoshin Tsaro

Ba zan kara yarda ana wa zaman lafiyar ’yan Najeriya cin kashi ba

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Manyan Hafsoshin Tsaro su cafko masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga su fuskanci hukunci.

Ya ba da umarnin ne a zaman Majalisar Tsaro ta Kasa, inda ya yi wa Manyan Hafsoshin Tsaro kashedi cewa ba zai kara yarda ’yan bindiga da masu satar mutane na yi wa zaman lafiyar Najeriya cin kashi ba.

Mashawarcin Shugaba Kasa kan Tsaro, Babagana Monguno, ya ce Buhari ya jaddada musu cewa hana ayyukan bata-garin ya kamata su yi, ba wai daukar mataki ba bayan miyagun sun riga sun tsula tsiyar tasu ba.

A yayin zaman na ranar Talata wanda bayansa Buhari zai tafi duba lafiyarsa a birnin London na kasar Birtaniya, ya jaddada cewa dukkannin matakan da Majsalisar ta dauka nan daram suna aiki.

Matakan sun hada da hana ayyukan hakar ma’adinai da haramta shawagin jiragen sama a Jihar Zamfara, da kuma umarnin harbe duk wanda aka gani rike da bindiga ba bisa ka’ida ba.