Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Manyan Hafsoshin Tsaro su cafko masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga su fuskanci hukunci.
Ya ba da umarnin ne a zaman Majalisar Tsaro ta Kasa, inda ya yi wa Manyan Hafsoshin Tsaro kashedi cewa ba zai kara yarda ’yan bindiga da masu satar mutane na yi wa zaman lafiyar Najeriya cin kashi ba.
- Yadda Zulum ya rage wa masu ice hanya da motar gwamnati
- Ganduje ya fitar da N8.9bn na gina Gadar Sama a Hotoro
- Fada a jirgi: Okorocha bai ga komai ba tukuna —Basarake
Mashawarcin Shugaba Kasa kan Tsaro, Babagana Monguno, ya ce Buhari ya jaddada musu cewa hana ayyukan bata-garin ya kamata su yi, ba wai daukar mataki ba bayan miyagun sun riga sun tsula tsiyar tasu ba.
A yayin zaman na ranar Talata wanda bayansa Buhari zai tafi duba lafiyarsa a birnin London na kasar Birtaniya, ya jaddada cewa dukkannin matakan da Majsalisar ta dauka nan daram suna aiki.
Matakan sun hada da hana ayyukan hakar ma’adinai da haramta shawagin jiragen sama a Jihar Zamfara, da kuma umarnin harbe duk wanda aka gani rike da bindiga ba bisa ka’ida ba.