✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hana ’yan adawa yin magana

A ’yan watannin da suka gabata Jam’iyyar PDP da gwamnatin da take da ita a matakin tarayya suna amfani da jami’an tsaro da dukiyar kasa…

A ’yan watannin da suka gabata Jam’iyyar PDP da gwamnatin da take da ita a matakin tarayya suna amfani da jami’an tsaro da dukiyar kasa a kokarin da suke yi na dakile ’yan adawa da kuma tilasta ’ya’yan jam’iyyar da suke da korafi kanta su mika mata wuya ala tilas.
Rikicin cikin gida a jam’iyya ko rikici a tsakanin jam’iyyun siyasa ba laifi ba ne a inda dimokuradiyya ke aiki, kuma darewar jam’iyya ba abu ne sabo ba. Amma tun lokacin da aka fara dambarwa a Majalisar Gwamnonin Najeriya (NGF), wadda a yanzu ta dare gida biyu, gwagwarmayar neman iko ta kara tsamari.   
bangare daya da ke da’awar halacci ya nuna ya fi yawan gwamnoni a cikinsa, kuma yyana karkashin Gwamnan Jihar Ribas ne Misa Roimi Amaechi; yayin da daya bangaren da ked a daurin gindin Shugaban kasa Goodluck Jonathan ke karkashin Gwamna Jonah Jang na Jihar Filato.
Rarrabuwar siyasar ta jawo dambacewa a tsakanin magoya bayan Shugaban kasa da wadanda a yanzu ake daukarsu a matsain ‘masu tawaye,’ lamarin da ya jawo tashin hankali, musamman a Jihar Ribas, inda zaman majalisar jihar ya zo karshe cikin rudani da tashin hankali a farkon bana.
 Wani abin da ke daga hankali shi ne tsoma hannun gwamnati wajen taushe ‘masu tawayen’ a baya-bayan nan ta hararar gidajensu a Abuja da ko yunkuri rusa su ko kwace takardun shaidar mallakarsu da Hukumar Bunkasa Birnin Tarayya (FCDA) ke shirin yi.
Sakamakon gazawar Jam’iyyar PDP da Fadar Shugaban kasa su dinke bangarorin Majalisar Gwamnonin, bayyanar wani bangare na PDP da ake kira Sabuwar PDP ga alama ya kara karfi ga kokarin da ake yi na kawo nakasu ga kamfe din da Doktta Jonathan ke yi na neman sake tsayawa takara na wani zango a zaben shekara 2015 mai zuwa.
Gazawa a yi amfani da ka’idojin jam’iyyar domin jawo hankalin wadannan gwamnoni Bakwai na PDP ‘masu tawaye,’ domin su kawo karshen goyon bayan da suke ba sabon bangaren, sai aka koma ga amfani da dabarun nuna karfi, wasu daga cikinsu ma sun saba wa doka, sannan galibinsu ma domin neman gindin zama ake yi.
Yanzu ga shi an yi amfani da ’yan sanda domin tarwatsa taron da wannan bangare da suke adawa da PDP da Gwamnatin Tarayya ya kira, kuma ba a nuna haka a matsayin tayar da zaune-tsaye ko abin da zai iya jawo tashin hankali.
Hukumomin tsaro kamar Rundunar ’Yan sanda wajibi ne su rika zama ’yan ba-ruwanmu a irin wadannan al’amura, babban hadari ne da ya saba wa ka’ida a rika daukar ’yan adawar siyasa a matsayin makiya kasa. Musamman abin da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ribas ya yi, babban abin bakin ciki ne, inda ya ba kansa wani iko har ma ya shallake na manyansa, domin ya ci zarafin Gwamnan Jihar, wanda a tsarin mulki shi ne babban jami’in tsaro na jihar.
An ba da rahoton cewa Kwamishinan ’Yan sandan ya janye jami’an tsaron da aka tura don kare Gwamnan, kuma akwai lokacin da ya ba da umarni a hana ayarin Gwamna daga shiga Gidan Gwamnati da ke Fatakwal.
Yanzu kuma ga Ma’aikatar Birnin Tarayya ta shawarci wasu sassa da ke karkashinta kan yadda za a dawo ‘masu tawayen’ kan hanya ko a hukunta su idan suka ki. Mako biyu da suka gabata ne jami’an ma’aikatar suka fahimci cewa Masaukin Gwamnan Jihar Adamawa da ke Abuja ana gudanar da wasu haramtattun ayyuka, don haka aka sa masa alama don rushewa. Jami’an ma’aikatar sun ce an mayar da ginin wurin kamfe lamarin da ya saba wa ka’idojin Hukumar Raya Birnin Tarayya (FCDA), kuma makwabta sun yi kukan ana yyawan damunsu da surutu sakamakon wadannan tarurruka. Gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako sananne ne mamba ne na ‘masu adawa na sabuwar PDP.’
Daga baya   an shaida wa wani mamba na rukunin wato Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso cewa, an kwace wani filinsa na Abuja. Kuma sakatariyar ‘Sabuwar PDP’ ta kasa an sat a a hanyar rushewa. Sannan wata sanatar PDP Hajiya A’isha Alhassan wadda ita ma ‘mai adawa’ ce kuma tana gudanar da wata cibiyar taro shekara da shekaru a Abuja, Hukumar FCDA na shirin kwace mata hakkin mallakarta.
Wannan irin mummunan martani ga abokan adawa ba abu ne mai kyau ba, kuma ba zai taimaka wajen raino da dorewar dimokuradiyyarmu ba. Adawa hatta a cikin jam’iyyu, abu ne da ake girmamawa shekara da shekaru kuma ya kamaa a ci gaba da haka, ba a rika ba ta mummunan suna da batunci ba kamar yadda jam’iyya mai mulki da gwamnati ke kokarin yi ba.