✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hana shigo da karamin janareto

Dokar Gwamnatin Tarayya ta hana shigo da kananan janareto, wadanda ake yi wa lakabi da “na dara makwafcina – I better pass my neighbor,” ya…

Dokar Gwamnatin Tarayya ta hana shigo da kananan janareto, wadanda ake yi wa lakabi da “na dara makwafcina – I better pass my neighbor,” ya haifar da cece – ku- ce daga dimbin masu ruwa da tsaki. Gwamnati ta ce haramcin ya zama dole saboda irin wadannan janareton suna gurbata iska da yi wa lafiya illa. Ba su kadai ya kamata zarga ba, injunan motoci da ke amfani da man dizil, har ma masu shan fetur da ba a kula da su tare da janaretoci masu shan dizil duk suna tattare da hadari ga lafiyar dan Adam, sanadiyyar hayakin da suke fitarwa. Nau’ukan karamin janareto kuwa, wadanda suka yadu da yawa a wurare, har da gidaje, sun sha halaka daukacin iyalai.
Sukar da ake yi wa wannan haramcin shi ne, gwamnati ta haramta wa talakawa hanyar samun wutar lantarki, ba tare da ta samar musu abin da zai maye makwafin abin da aka kwace musu ba. Sun yi takaddama akan cewa, akwai bukatar gwamnati ta inganta wutar lantarki kafin ta aiwatar da wannan haramcin. Gaskiya ce a bayyane cewa, miliyoyin masu karamin karfi ke amfani da irin wadannan janaretocin, kuma suna taimakawa a harkokin neman abinci da suka hada da kananan harkokin kasuwanci a maciyar abinci da shagunan askin baba da kananan ofisoshi da kantunan sayar da kayayyaki da masu cajin wayar salula a biya su, har ma a dakunan kwanan dalibai da gidan zaman dimbin iyalai. A bayyane yake cewa, kowace karamar harkar kasuwanci na ta’ammali da irin wannan janareto a irin wannan lokaci da ake fama da matsalar wutar lantarki tsayayya. Irin wannan yanayi haka yake a yankunan karkara, inda mutane ke dogaro da nau’ukan wannan janareto wajen noma da amfanin gida da kananan harkokin kasuwanci.
Ganin cewa, hanin bai shafi shigo da manayan nau’ukan janareto ba, abin la’akari shi ne, masu karamin karfi ba za su iya sayen nau’ukan da ba a haramta ba. kananan harkokin kasuwanci da ake gudanarwa a birane da garuruwa za su iya shawo kan matsalolin su ta hanayar hada karfi su mallaki babban janareto don amfanin bai daya. Yin hakan ya fi musu saukin kashe kudi da kariyar lafiya ga kowa, tunda za a samu raguwar gurbacewar iska da kara da suka yawaita a kasuwanni, inda a yau kowa ke amfani da na shi ko nata karamin janareton. Abin da kawai ake bukata shi ne hadin kai a tsakanin masu amfani da shi.
Ita kuwa kungiyar Masu masana’antu ta Najeriya (MAN) da sauran ’yan kasuwa sun yi nuni da cewa, harmcin zai kara yawan marasa aikin yi a kasar nan. Sun ce kera karamin janareto mai nagarta a kasar nan zai yi wuya saboda tattalin arzikin mu bai yi nuni da tallafawa wajen saka hannun jari a babbar masana’anta ba. Sai dai wannan hanin na nuni da cewa za a samu yawan aiki ga dimbin masu gyara na wucin gadi, inda za a yi ta kawo musu tsofaffin janaretoci, tunda babu sababbi.
Ganin cewa an kyale masu kudi su ci gaba da amfani da manyan janareto masu shan dizil, sannan ga talakawa za su rasa hasken lantarki, akwai bukatar shawo kan matsalar. Hukumomi sun nuna cewa, dokar ba a gindaya sharadin farawa daga kan wadanda aka shigo da su ba. Haramcin bai shafi wadanda ake da su ba, don haka ana iya ci gaba da sayar da su. Jami’an hukumar hana fasakwauri na Kwastam sun tabbatar cewa, “haramcin  na kasuwanci ne,” domin dimbin jareton da aka shigo da su kawai za a kwace, ba ’yan kadan ba.
Don nuna goyon bayan mu ga wannan hanin, Injiniyoyi sun ce mu rika amfani da nau’ukan janareto da ake zuba musu fetur, wanda aka gauraya da bakin mai. Wannan man ne da ke konewa ke haifar da dimbin hayaki. Akwai dimbin kananan janareto wadanda ba a yi musu gauraye da bakin mai, amma ba su da tsada sosai. Iri wadanann nau’ukan ba a haramta su ba.
Duk da cewa muna goyon bayan wannan mataki da aka dauka don kare lafiya da hana gurbata iska, ya kamata tsarin ya zamo managarci wajen kare muhalli. Alal misali, gwamnati ta fuskanci hana kona iskar gas, wadda ta fi cutarwa ga muhalli da gurbata sararin samaniya a matakin “Ozone (ozone layer). daya daga cikin suka mai ma’ana game da haramcin shigo da kananan janareto, ita ce, ba a wayar da kan al’umma ba. Ganin yadda ake yawan amfani da nau’ukan karamin janareto a kasar nan, ya kamata al’ummar kasa su san manufar gwamnati kafin ma a aiwatar da hanin shigowar. Uwa-uba, muna sa ran ganin an samu ci gaba mai alfanu wajen samar da wutar lantarki nan ba da dadewa ba.