A makon jiya ne Sakatariyar Harkokin Sufuri ta Babban Birnin Tarayya Abuja ta fitar da wani jadawali wanda ke fayyace ka’idojin aiki da motocin daukar masinjoji a Abuja. Sakataren Sufurin, Kayode Opeifa ne ya bayyana haka, jim kadan bayan kammala wata tattaunawa da suka yi da dukkan masu motocin haya da aka yi wa rajista a birnin, inda ya ce wajibi dukkan kananan motoci da manyan bas-bas da kanana da kuma Keke Napep su mallaki lambar mota mai kalar ja.
Opeifa ya ce, “Wajibi ne dukkan motocin haya manya da kanana da keke su yi rajistar jar lamba, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga Watan Oktobar wannan shekara. Sannan kuma wajibi ne dukkan motocin da suka yi rajistar yin jigilar fasinjoji su kasance masu dauke da na’urar sanyaya mota kafin nan da ranar 1 ga Watan Oktobar a fadin Abuja baki daya. Kamar yadda yake wajibi gare su, su samu takardar shaidar na’ura mai aiki da taswira don haska duk inda motar haya ta ke wanda za a rika sauya wa’adin a duk bayan watanni tara.”
Sakataren ya kara da cewa, dole ne dukkan direbobin motocin hayar su mallaki lasisin tuki wanda kuma zai samu tantancewa daga sakatariyar sufurin bisa dokokin birnin tarayyar. Haka kuma ya ce wajibi ne dukkan wadanda aka yi wa rajistar su nuna takardun shaidar biyan haraji a Abuja. Sai ya ce za a bada izinin shiga ko’ina ga wadanda suka cika ka’idojin da suka hada da manyan otal-otal da rukunin gidaje da manyan ofisoshin gwamnati.
Babban fa’idar da wannan tsari ya kunsa shi ne na samun kudaden haraji da babban birnin ya samu nasarar tarawa idan shirin ya kankama. Misali; abin da ya shafi rajistar sababbin lambobin motocin hayar ga dukkan bangarorin motocin hayar da aka lissafa, da takardun shaidar na’urar taswirar da za ta haska duk inda motar haya ta ke, da biyan kudaden haraji ga masu haya da motocin sannan da kuma rajistar dukkan motocin hayar abu ne da zai kara bunkasa hanyoyin samar da kudaden shiga ga Babban Birnin Tarayya Abuja.
Amma wani babban abu da yake ci wa mazauna birnin tuwo a kwarya bai wuce yadda za a magance rashin bin dokar motocin hayar da kuma gudun ganganci ba. Haka kuma mazauna birnin za su samu natsuwa muddin za a magance matsalolin dauka da sauke fasinjoji barkatai akan titunan Abuja, lamarin da kan haddasa tsaiko ko toshewar hanyoyi a kullu yomin. Haka nan a samu kyakkyawan tsari ga su ma masu ayyuka da Keke Napep musamman akan hahadar da fitilu kan bada hannu.
Haka kuma sakataren ya ce tuni aka jingine batun nan na samar da lasisin gudanarwa, sai ya bada umarnin cewa ba za a bada wata dama ga tsofaffin masu rajista wajen ci gaba da ita ba, amma suna damar sake yin biyayya ga sabon tsarin. Kamar yadda dokokin suka nuna, za a gabatar da dukkan sunaye da yawan motocin hayar da kowane yanki ke da su ga sakatariyar kafin zuwa ranar 13 ga Watan Afirilun da ya gabata. Wannan kuma don saukaka harkokin gudanarwa da ayyukan bincike da kare hadurra da kuma samar da cikakken tsaro a birnin. Sannan ya umarci dukkan wadanda shirin ya shafa da su hanzarta zuwa cibiyoyin sufuri da fara shirye-shiryen rungumar sababbin dokokin.
A yayin da muke jinjina wa Hukumar Birnin Tarayya bisa kokarinta na tsaftace birnin daga dukkan abin da zai kuntata rayuwar al’umma, muna kuma jan hankalinta zuwa ga batun nan na cewa dukkan mai aiki da motar haya sai ya sanya na’urar sanyi a motarsa kafin ba shi izinin daukar fasinja, gaskiya babu bukatar wannan doka a halin yanzu sam. Abin dubawa game hakan shi ne akwai motocin da ake jigilar fasinjojin da ba su da nagartattun tayoyi wasu ma babu cikakken burki wasu kujerun zama a cikin motocin sun rube da sauran abubuwan da suka kamata ace hukumar ta fi mayar da hankali kan su fiye da wannan doka da sanya na’urar sanyaya mota.
Fasinjoji za su fi bukatar isa ga wuraren da suka nufa cikin lumana duk kuwa da zafin rashin na’urar sanyi, a maimakon shiga motocin masu sanyi cikin fargabar rashin ingancin taya ko burki. Baya ga wannan ma, wata matsalar da ta fi addabar al’umma a birin na Abuja ita ce ta shiga motocin barayi da aka fi sani da ‘one chance’ fiye da rashin na’urar sanyi a mota. Don haka muna kira ga mahukuntan harkokin sufuri na Abuja su sake duba wannan doka wacce alfanunta ba mai yawa ba ne, idan aka yi la’akari da mafiya muhimmanci daga cikin wadanda muka ambata a baya.