✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hamas ta yi barazanar kashe Isra’ilawan da ta yi garkuwa da su

Ana zargin cewa dakarun Isra’ila sun kashe ’yan Hezbollah uku.

Kungiyar mayaƙan Hamas ta Falasɗinu ta yi barazanar kashe Isra’ilawa akalla 150 da take garkuwa da su saboda hare-haren da ake kai wa Zirin Gaza.

Wannan na zuwa ne bayan da Isra’ila ta sanar da yi wa baki ɗayan Gaza ƙawanya a yayin da faɗa ke ci gaba da ruruwa tsakaninta da kungiyar Falasɗinawa ta Hamas.

“Na ba da umarnin a yi wa Gaza ƙawanya ruf,” a cewar Ministan Tsaron Yoav Gallant bayan wani taron tattaunawa kan lamarin, a cewar shafin Jaridar Times of Israel.

“Ba za mu samar musu da wutar lantarki da ruwa da abinci da man fetur ba, an rufe Gaza ruf,” Gallant ya ƙara da cewa.

Ministan Makamshi na Israi’ila Katz shi ma ya bayar da umarnin katse hanyoyin samar da ruwan sha zuwa Gaza, kamar yadda mai magana da yawunsa ya fada a wata sanawa.

Umarnin Katz na zuwa ne jim kadan bayan umarnin Gallant na rufe Gaza ruf, wacce ke samun kusan kasi 10 cikin 100 na ruwan shanta daga Isra’ila.

Da safiyar ranar Litinin, rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa ta kai hare-hare wurare 500 kan Gaza cikin dare, tana mai ikirarin cewa wuraren maɓoyar Hamas da masu ikirarin jihadi ne.

Ƙungiyar Hamas mai cibiya a Gaza ta ƙaddamar da hari kan Isra’ila a ranar Asabar, ta hanyar harba rokoki.

Ta ce ta yi harin ban mamakin ne a matsayin martanin ga kutsen da Isra’ila ke yi wa Masallacin Ƙudus da kuma mamayar Yammacin Kogin Jordan da ke ƙaruwa.

Ita ma Isra’ila ta mayar da martanin ta hanyar kai hare-hare kan Hamas a Zirin Gaza, inda Falasɗinawa 560 suka mutu sannan aƙalla 2,751 suka jikkata.

Aƙalla ’yan Isra’ila 800 aka kashe kuma fiye da 2,300 suka jikkata a yaƙin, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Isra’ila.

Martanin Isra’ila kan Hamas zai sauya Gabas ta Tsakiya — Netanyahu

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce martanin Isra’ila kan Hamas a Gaza zai “sauya Gabas ta Tsakiya.”

Yana magana ne ga rukunin magajin garin garuruwan da ke kan iyakar kudancin kasar waɗanda hare-haren ranar Asabar ya shafe su, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa.

Sai dai bai yi ƙarin bayani ba a kan hasashen nasa.

Hamas ta ƙaddamar da harin da ta kira Operation Al Aqsa Flood a kan Isra’ila da safiyar ranar Asabar, inda suka harba rokoki.

Ta ce harin shammata martani ne kan afka wa Masallacin Ƙudus da kuma ci gaba da mamayar Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ke yi.

A martanin da ta mayar, rundunar sojin Isra’ila ta ƙaddamar da harin da ta kira Operation Swords of Iron.

Ta kai hare-hare kan wurare 500 cikin dare a Gaza, waɗanda ta ce na ƙungiyar Hamas da ƙungiyoyi masu da’awar Jihadi ne.

Ana zargin Isra’ila da kashe ’yan Hezbollah uku

Kamfanin Dillancin Labaran na Faransa AFP ya ruwaito cewa wani hari da Isra’ila ta kai kan wata hasumiyar sintiri ta Lebanon ya yi sanadin kashe wasu ’yan ƙungiyar Hezbollah uku a ranar Litinin.

A cewar ƙungiyar a yayin da ake ci gaba da kai hare-haren bayan da wasu mayaƙan Falasdinu suka yi ƙoƙarin kutsawa Isra’ila daga Lebanon.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce sojojinta sun kashe wasu mayakan da ake zargi da dama, wadanda suka shiga yankinta daga Lebanon kuma helikwaftanta yana shawagi da sa ido a yankin.