“Sun kawo wata mata ta rika girka mana abinci (mu 300), kuma abincin ma ba kyauta ba ne, dole sai ka saya.
“Hatta a watan azumi na Ramadan da mutane ke bukatar nau’o’in abinci iri-iri don buda-baki, shinkafa da taliya kawai suka rika danna mana.
“Mun fuskanci wulakanci da cin mutunci iri-iri, amma ba yadda muka iya.
“Wani mai shayi kawai aka bari ya shigo yake sayarwa a kamfanin, ban da shi ba wani abin da za ka iya saye a waje, ba ka da dama”, inji Alhaji Yahaya.
- Kamfanin shinkafar Kano ya ci gaba da aiki duk da samamen ‘yan sanda
- Yadda aka ceto leburori 126 da aka kulle wata uku a wata masana’anta
Kadan ke nan daga irin bayanan da wasu daga cikin ma’aikata 126 da ’yan sanda suka yi nasarar kubutarwa daga kullen da wani kamfanin sarrafa shinkafa mai suna Popular Rice Mill a Kano ya yi musu na tsawon wata uku.
Alhaji Yahaya, daya daga cikin leburorin da aka kulle a kamfanin, ya bayyana halin da suka tsinci kansu a kamfanin da cewa yana da kamanceceniya da na bayi.
Kamfanin, wanda rahotanni suka nuna cewa mallakar wasu Indiyawa ne, an zarge shi da kulle ma’aikatan na tsawon wata uku ba tare da barin su suna fitowa ko da kofarsa ba, saboda fargabar kada su kamu da cutar coronavirus bayan ta fara bulla a jihar Kano.
A wata tattaunawa da Aminiya, Alhaji Yahaya, wanda daya ne daga cikin jagororin leburorin, ya ce ya shafe kimanin shekaru uku yana aiki a kamfanin a matsayin kwantiragi.
‘Saba alkawari’
Ya kuma zargi kamfanin da gaza cika alkawuran da ya yi musu bayan ajiye su suna masa aiki ba dare ba rana na tsawon watanni uku.
“Sun kulle mu a nan muna ta aiki na tsawon watanni uku ba tare da ko fitowa waje ba, balle maganar ganin iyalanmu duk da cewa da yawa daga cikinmu muna da aure.
“Kuma ko masallaci babu a ciki ballantana mu rika yin sallar Juma’a ko ragowar salloli”, inji shi.
‘Ba tsarin kula da lafiya’
Ta bangaren kiwon lafiya kuwa, ya ce kamfanin bai yi wani tanadi ba wajen kula da su.
“Duk wanda rashin lafiya ya kama sai dai ya nemo yadda za a shigo masa da magani ta barauniyar hanya ba tare da masaniyar hukumar kamfani ba.
“Sai dai mu aiki ma’aikatan da suke aikin fitar da dusa daga kamfani su sayo mana magani a boye.
“Akalla mutum 20 daga cikinmu sun yi rashin lafiya amma babu wata hobbasa da kamfanin ya yi ta kula da su ko kai su asibiti”, inji Alhaji Yahaya.
Mukhtar Abubakar ma daya ne daga cikin leburorin. Ya ce, “Akwai ma daya daga cikinmu da injin kamfanin ya yi masa rauni amma ba abun da suka yi masa, haka ya yi ta fama har ya warke.
“Ta bangaren makwanci kuwa, kawai wata katuwar fafaranda suka ware mana da tabarmi. Haka muka rika rayuwa kamar bayi.
‘Idan ana ruwa ba barci’
“Idan ana ruwa kuma, wajen zuba yake yi, ba damar yin barci ko kadan. Haka muka yi ta rayuwa har tsawon watanni ukun.
“Abin da ma ya fi kona min rai shi ne yadda kamfanin ya ce wai yana ba mu N5,OOO duk mako, wannan ba gaskiya ba ne.
“Ko sisin kwabo ba a kara mana ba [a kan] albashinmu”, inji Abubakar.
Leburorin sun kuma bayyana cewa suna fargabar kamfanin zai sallame su daga aiki saboda wai sun yi yawa.
Damar ganin iyali
Da Aminiya ta tambaye su ko sun samu zarafin ganin iyalansu yayin kullen, Alhaji Yahaya ya ce sam, sai dai kawai su aika musu da kudi.
“Sai dai kawai ka kira daya daga cikin ’yan uwanka su zo, sai ka ba masu gadin kamfani su ba shi a boye, amma ba za ku ga juna ba.
“Ni iyalai na alal misali na zaune ne a unguwar Kofar Ruwa amma tsawon watanni ukun nan ba mu ga juna ba, sai dai kawai na aike musu da kudi”, inji shi.
‘Abincin ba dadi…’
Aminiya ta kuma tattauna da wasu masu shaguna masu makwabtaka da kamfanin inda ma’aikatan ke sayayya kafin a kulle su.
Salmanu Musa, wani mai shagon sayar da kayan waya a kusa da kamfanin, ya ce duk lokacin da ma’aikatan ke bukatar wani abu kamar katin waya ko taba sigari sai dai su yi waya a shigar musu da kayan ta barauniyar hanya ta hanyar ba masu gadin kamfanin cin hanci.
“Sukan kira mu in suna bukatar wani abu, amma dole sai mun ba masu gadi ‘na goro’ kafin su amince su kai musu.
“Sun kuma sha yi mana korafi lokacin suna ciki cewa abincin da ake ba su ba ya wadatar da su kuma ba dadi”, inji Musa.
‘Matsayin bayi’
Leburorin sun kuma koka da abin da suka kira wulakanci daga shugabannin kamfanin.
“Na shafe sama da shekara 10 ina aiki a nan, muna tara musu kudi. Wani lokacin, biyan mu hakkokinmu ma yakan zama jidali.
“Idan mutum ya dauki babban buhun gyada wanda sai mutum shida sun taru kafin su dora maka, misali, N35 za a baka, yayin da karamin buhun shi kuma suke biyan N20. Haka muka yi ta rayuwa”, inji wani mai suna Yunusa.
Sun kuma yi zargin cewa kamfanin na daukar su a matsayin bayi duk da cewa in babu su ba zai aiki ba.
Hira da ’yan jarida
A wani labarin kuma, daya daga cikin leburorin da ya yi magana da Aminiya bisa sharadin sakaya sunansa ya ce biyu daga cikinsu sun shafe yinin ranar Alhamis suna amsa tambayoyi a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan Sanda don kawai sun yi hira da ’yan jarida.
Ya yi zargin cewa kamfanin ne ya kai su kara bisa zarginsu da yunkurin bata masa suna.
“Yanzu haka sama da mutum 200 daga cikin abokan aikinmu na can suna watayawa amma su wadannan mutum biyun sun fada tsaka mai wuya”, inji shi.
Har yanzu bincike ake
To sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce har yanzu suna ci gaba da bincike kan lamarin, da zarar sun kammala kuma za su sanar da jama’a.
Da yake tabbatar da lamarin, daraktan kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Global Community for Human Rights Network, Karibu Yahaya Lawan Kabara, ya ce yanzu haka batun na gaban ’yan sanda.
A cewarsa, “Ko a jiya (Alhamis) sai da Kwamishinan ’Yan Sanda ya kira mu kan lamarin, sai dai har yanzu muna da wata matsala da wannan kamfanin; har yanzu sun ma ki su yarda sun aikata laifi.
“Akwai wani daga cikinsu da sunansa ya fita a jarida kamfanin ya sha alwashin sai ya hukunta shi, sai da muka je har gaban Kwamishinan ’Yan Sanda da shi ranar Alhamis”, inji Yahaya.
A kan matakin da za su dauka kan kamfanin nan gaba, daraktan ya ce ’yan sanda na ci gaba da bincike kuma sai sun kammala tukuna kafin su yanke shawara.
‘Gaskiyar abin da ya faru’
Da Aminiya ta tuntube shi, manajan sashen mulki na kamfanin, Kareem Saka, ya musanta duk zarge-zargen da aka yi musu.
A cewarsa, “Ranar Litinin da ta gabata, kungiyar Global Community for Human Rights Network da ’yan sanda sun yi wa kamfaninmu kawanya suka iske wasu leburori suna shan iska sai suka kwashe su…amma ba a fi minti goma ba da yawa daga cikinsu suka fara dawowa suna cewa ba za su tafi su bar abin da suke samu a wajen ba.
“Kusan duk ma leburorin da ake magana a kansu ba ma’aikatanmu ba ne, wani ne ya dauke su kwantiragi.
“Amma duk da haka mun ci gaba da biyansu cikakkun hakkokinsu, kai har ma da karin N5,000 a kowanne wata (ta hannun wadanda suka dauke su aikin).
“Ba wanda ya ke kwana a fafaranda a cikinsu, mun samar musu da dakuna.
“Yawancinsu ba wai cikakkun ma’aikata ba ne, saboda haka kullum muke biyansu ba wata-wata ba. Sukan sami abin da ya kai daga N2,000 zuwa N6,000 a kullum.
“Yanzu haka maganar da nake yi da kai yawancinsu sun dawo bakin aikinsu. Idan zaluntarsu muke yi ko daure su muka yi, za su dawo?
“Kawai dai mun fahimci wani ne a wani wajen ya ke kokarin bata wa kamfaninmu suna duk kuwa da yadda muke kokari wajen samar wa mutane ayyukan yi tare da kiyaye ka’idoji”, in ji Saka.
‘Muna bincike kan lamarin’
A nata bangaren kuwa, kungiyar kwadago ta kasa reshen jihar Kano ta koka da cewa kamfanin ya ki barin leburorin su yi kungiya.
Shugaban kungiyar, Kwamared Kabiru Ado Minjibir, ya ce tuni su ka fara bincike don gano gaskiyar lamarin, yana mai cewa za su tsaya tsayin daka wajen ganin sun kwato wa ma’aikatan hakkokinsu.
Ya kuma ce muddin kungiyar ta gano kamfanin ya tauye wa leburorin hakki, to tabbas za su bukace shi da ya biya diyya.