✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halima M. Musa

Dokta Fatima Othman, it ace  Daraktar Linkages, Kamfanin Zuba Jari Na Jihar Nasarawa wacce ofishinta ke hade da na Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa (bice…

Dokta Fatima Othman, it ace  Daraktar Linkages, Kamfanin Zuba Jari Na Jihar Nasarawa wacce ofishinta ke hade da na Mataimakin Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa (bice Chancellor) da ke Keffi na Jihar Nasarawa.  Aminiya ta tattauna da ita inda ta ji fadi-tashin da ta yi da kuma nasarorin da ta samu a rayuwa kamar haka

Tarihin rayuwa:
Sunana Fatima Othman.   Na yi karamar makaranta a Katsina don mahaifiyata bakatsiniyace, mahaifina kuma dan Nasarawa ne amma duk ayyukan da ya yi a  Katsina ne.  Sannan na wuce Kwalejin da ake kira Probincial Girls Cchool amma yanzu ana kiranta WTC Katsina.  A wancan lokaci ina daga cikin masu kokari don na so na karanta likitanci amma sai aka dauki masu kokari aka kaimu don mu koyi karantarwa don mu fito malamai.  Na fara koyar wa a Jihar Kano don a lokacin maigidana yana aiki a can.  Na yi aure ne tun lokacin da na kare karamar makaranta ta aji bakwai.  Karatun Grade 2 a gidan mijina na yi don a lokacin ma na haifi ’ya’ya uku.  Na yi Adbance Teachers’ College Zariya daga nan na zarce  Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya.   Na yi koyarwa na shekara daya.   Bayan haka a lokacin da nake da ’ya’ya biyar ne na gama digirina na farko.   Na yi bautar kasa a Jos don a lokacin maigidana ya koma da aiki a can.   An dauke dauke ni aiki a wurin.  Daga nan na yi digiri na biyu (Masters) a wata Jami’a a Landon da kuma digirin-digirgir PHD a Paris.   Na dawo Najeriya na cigaba da koyarwa a Jami’ar Jos. Na rike mukamai da yawa a kasar nan.  Na sake komawa Paris inda matsayin mai koyawara a wata Jami’a.   Ni ce wakiliyar Najeriya a Asusun Tallafawa Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNESCO).  Na yi shakara takwas a can da kuma karin wasu shekaru biyu, goma ke nan.   Bayan na yi ritaya sai na dawo Najeriya, kuma a yanzu ni ce Daraktar Hukumar kula da zuba jari ta Jihar Nasarawa da aka fi sani da Linkages na Jami’ar  jihar Nasarawa.
Yaya kika ga cigaban ilimin mata a arewacin najeriya?
Yanzu dai kam godiya ta tabbata ga Allah saboda ba kamar da ba, yawancinmu tun da muna da ilimi, dole mu sa y’ya’yanmu a makaranta.   Da ma wurin da ake samun tangarda shi ne idan iyaye ba su da ilimi, sai a yi ta azawa yara talla, wannan abu ne wanda bai dace ba,  ana gudun wai kada yaro ya lalace a makaranta ba a san kuma yin tallar ya fi aibu ba.   Wannan yana nakasa yara sosai, don cikin masu tallar akwai masu kwazo a fannoni daban daban da zai amfani rayuwar mu amma sai a yi ta asarar haka ta hana su zuwa makaranta, ana aza masu tallar da ba za ta tsinana musu komai ba a rayuwar su.   Wannan shi ne abin da ke sanya mu samu koma-baya sosai.  Na biyu kuma wasu ba su da halin da za su sanya ’ya’yansu a makaranta ne saboda halin kuncin rayuwa.
Wace hanya kike ganin za a iya bi don shawo kan wannan matsala?
Idan zai yiwu Gwamnati ta dauki ilimin mata da gaske.   A da, mutum na biyan kudin makaranta ne ta yadda samunsa yake.   Ida manomi ne, za a yanka masa kudin da zai biya wa yaransa na makaranta ne daidai samun sa.   Idan ilimi ya wadatu mutanen Arewa ko auri- saki din nan da ya yi yawa a Arewa zai ragu matuka.
Wadannen kalubale ki ka fuskanta?
kalubalen da na  samu shi ne a lokacin da zan tafi karo karatu a Landan.  Mijina ya dan nuna rashin yardarsa, amma daga baya komai ya tafi daidai.
Ya kike hada aikin ofis da rayuwar aure?
 A gaskiya akwai wahala kwarai da gaske sai mace ta dage.

Akwai riba a tare da mace mai ilimi – Dokta Fatima Othman

Me kika fi so?
 A gaskiya na fi son tafiye- tafiye don yana kara ilimi.   Na je kasashe da dama.  A lokacin da nake aiki da UNESCO na tsawon shekaru 10 mun je kasashe sun fi goma, don idan zamu yi taro ba ma yi a Paris sai dai mu je wata kasa, don a UNESCO akwai kasashe 191.  Sannan abu na biyu da na fi so shi ne yin karatu da kula da yara.
Me ya fi bata miki rai?
Abin da ya fi bata mini rai shi ne in ga yara mata suna talla a kan hanya.  Sannan ban kaunar na ga mata na shan wahala. A kasar Turai sukan tallafa wa marasa karfi don su je makaranta, amma abin ba haka yake a nan gida Najeriya ba.
Mene ne burinki a rayuwa ?
 Burina shi ne na ga kowace mace ta samu ingantaccen ilimi, don ilimi shi ne ginshikin komai na rayuwa.
Me za ki iya cewa game da siyasar mata a kasar nan?
Ni abin da na fi so ga mata shi ne, kada su yi shakkar komai, su shiga harkokin siyasa a dama da su, amma su rike mutuncinsu, su kama kansu.  Idan ba mu shiga harkokin siyasa ba, ta yaya za mu iya kare mata yan’uwanmu?  amma dai mu yi haka cikin mutunci da kamun kai.  Idan masu ilimi ba su shiga harkokin siyasa ba aka bar wadanda ba su da ilimi, bai fi a ba su shugaban mata ba kawai (Women Leader). Amma idan kina da ilimi kika shiga siyasa za ki samu matsayin da  ya dace don mu rika tallafa wa mata ’yan’uwanmu musamman marasa karfi.
Wace shawara gare ki ga mata ’yan arewa?
Shawarata ita ce su tashi tsaye wajen yin sana’a ko aiki da kuma neman ilimi.  Ilimi shi ne ginshikin da zai sa a samu cigaban al’umma.  Ina kuma rokon maz su taimaka wa matansu don su samu ilimi, domin yawanci maza su ke hana matansu neman ilimi.   Idan mace ba ta da ilimi, zamantakewar aure ma zai zame mata matsala amma idan akwai ilimi za ku ga komai na tafiya daidai.