✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halawa mai gyara fata

  Halawa wata aba ce da ake amfani da ita wurin gyaran fatar jiki ce. Wannan halawar an fi samunta a Jihar Barno. Akan hada…

 

Halawa wata aba ce da ake amfani da ita wurin gyaran fatar jiki ce. Wannan halawar an fi samunta a Jihar Barno. Akan hada ta musamman ga amare. Akan hada ta ne ta hanyar amfani da siga da lemun tsami da ruwa kadan. Wannan halawar na amfani wurin debe gashin fata domin ta yi sulbi da laushi.
Abubuwan da ake bukata:
·        Cokali 3 na siga ko zuma
·        Lemon tsami 3
·        Ruwa cokali daya
Yadda ake hadawa:
A dora tukunya a murhu idan ta yi zafi sai a zuba siga ko zuma, idan siga ko zuma ta fara narkewa sai a zuba lemon tsami da ruwa kadan. Idan a murhun itace ne ake hada halawar to kada a bari wutar ta kama sosai, haka idan ma da risho ne ko na’urar gas cooker da sauransu. Domin kada ta kone. A yi ta gaurayawa zuwa minti 45 har sai hadin ya koma ruwan kasa, sannan a sauke. A jira ta huce. Za a ga ta yi danko. Sai a samu cokalin katako ko na roba a shafa a kan fata inda akwai gashin jiki. Bayan ya bushe, sai a sami tsumma a danna a kan fata sai a rika ciro ta. Yin hakan na fitar da gashin fata kuma za a ga fatar ta yi sulbi da santsi.