Godiya ta tabbata ga Ubangiji Allah Mai iko duka. Barkanmu kuma da sake saduwa a wannan makon.
A wannan mako za mu yi nazari a kan muhimmancin hakuri a rayuwan mai bin Yesu Almasihu.
Ba sai an gaya maka cewa a yau mutane da dama sun zama marasa hakuri ba; yin hanzari domin samun biyan bukata ta kowace hali ba tare da tunanin ko kana cin zarafin wani ba, don rashin hakuri mutane kan yi kisa, kwace, fashi, sata, zalunci don neman biyan bukata. Wadansu ma har sun shiga halin sayar da jariran da suka haifa, ko sace na wani don neman yin dukiya ko samun mukami a gaggauce. Mene ne ke kawo irin wannan? Littafi Mai tsarki na cewa “Kauna tana sa hakuri da kirki. Kauna ba ta sa kishi, ba ta yin kumbura. Kauna ba ta sa daga kai ko rashin kara, kauna ba ta sa son kai, ba ta jin tsokana, ba ta riko. Kauna ba ta sa yin farin ciki da mugunta, sai dai da gaskiya. Kauna tana sa daurewa a cikin kowane hali, da ban-gaskiya a cikin kowane hali, haka kuma sa zuciya a cikin kowane hali da jimiri a cikin kowane hali.” (1 Korantiyawa 13:4-7). Rashin kauna kan haifar da son kai da mugunta da rashin hakuri wanda zai kai mutum ga hallaka na har abada.
Kada kuma wani ya samu dalilin cewa ai ba ni da irin wannan hali a ruyuwata, yin fushi na daya daga cikin irin wannan hali, mu duba dai a duk lokacin da mutum ya fusata da wani ko wani abu, za ka ga mutane na kokarin cewa; Ka yi HAKURI! Sai HAKURI! Idan har ya yi hakuri sai ka ga cewa an samu salama da zaman lafiya da kauna, amma idan bai yi hakuri ba, sai ka ga fushin ya kai shi ga yin kisa, ko wata barna da za ta kawo wahala “Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.” (Karin Magana 14: 29). Ashe yin hakuri kan magance irin wannan hali. Shi ya sa hakuri na daya daga cikin albarkar ruhu da ya kamata mu zama muna da shi a koyaushe a cikin rayuwar nan da Allah Ya ba mu. Littafi Mai tsarki na cewa: “Ya fi kyau ka zama mai hakuri da ka zama mai karfi. Ya fi kyau ka iya mallakar kanka fiye da mallakar birane.” (Karin Magana 16:32).
Yin hakuri cikin zamaninmu na yanzu ba abu ne da ke da sauki ba, mutane na da halin cakuna, idan har sun ga kana kokarin neman zaman lafiya. Suna yin haka ne don ba su san Ubangiji Allah ba, da sun san Shi, za su bi abubuwan da Ya fadi cikin littafinSa mai tsarki. Luka 10:25-28; “Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?” Yesu ya ce musu, “Me yake rubuce a Attaura? Yaya kake karantawa?” Sai ya amsa ya ce, “Ka kaunaci Ubangiji Allah da dukkan zuciyarka da dukkan ranka da dukkan karfinka da dukkan hankalinka. Ka kuma kaunaci dan uwanka kamar kanka.” Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka rika yin haka, za ka rayu.” Sanin Ubangiji yakan sa ka kaunace Shi da dukkan zuciyarka da dukkan ranka da dukkan karfinka da dukkan hankalinka, yin haka kuma zai sa ka kaunaci dan uwanka kamar kanka, kaunar dan uwanka kuma zai sa ka zama da hakuri, inda aka samu hakuri kuma a nan za a samu salama da farin ciki da kauna. “Saboda haka, sai ku dauki halin tausayi da kirki da tawali’u da salihanci da hakuri, idan ku zababbu ne na Allah, tsarkaka, kaunatattu.” (Kolosiyawa 3:12)
Ban da rashin hakuri da juna, wadansu mutane a yau suna nuna rashin hakurinsu ga Ubangiji Allah, ba su da hakurin jiran lokacin da Ubangiji Ya sa abubuwa su faru a rayuwarsu, son kai da kishin juna ya mamaye tunaninsu, idan makwabcinsu ya gina gida ko ya samu abin hannu, sai ka ga cewa su ma suna son su samu wannan abin ko ta wane hali. Ba sa tunanin mika damuwarsu ko bukatunsu ga Allah Mai biyan bukatar kowa da kowa, Allah kadai Ya san zuciyar mutum, Shi ya san jiya Ya san yau da kuma nan gaba. Ubangiji ba Ya jinkirta alkawarinSa, yadda wadansu suka dauki ma’anar jinkiri, amma mai hakuri ne a gare ku, ba Ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba. (2 Bitrus 3:9). Me zai hana ka dogara ga Mahaliccinka wanda Ya san komai da komai don biyan bukatunka? Ba a rana daya aka hallice mu ba, ba kuwa kamanni daya muka zo da shi ba, haka nan lokutan da Ubangiji Allah Ya sanya mana sun bambamta, rashin sanin cewa Ubangiji Ya san komai bisa rayuwarmu kan sa mutum ya zama mara hakuri, shi ya sa za ka ga mutane na zuwa wurin kowane mutum da ya kira kansa fasto, ko gidan addu’a domin neman biyan bukatar kai (dukiya, aure, haihuwa, gida, mota da sauransu), amma ba don neman sanin Ubangiji ba. Domin idan har ka san Ubangiji Allah kana kuma kaunarSa kamar yadda Ya fada a cikin maganarSa babu shakka za ka bi tafarkinSa kuma za ka zama da hakurin jiran nufinSa bisa rayuwarka.
Sai mu yi lura, kada mu bar rashin hakurinmu ya sa mu gaba da Ubangiji da kuma ’yan uwanmu, mu roki Ubangiji Ya cika mu da albarkar ruhunSa na kauna don mu zama masu hakuri da nufinSa da juna kuma. Kamar yadda Manzo Bulus ya rubuta. “Don haka, ni dan sarka saboda Ubangiji, ina rokonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku da matukar tawali’u da salihanci da hakuri, kuna jure wa juna saboda kauna.” (Afisawa 4:1,2).