✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakora: Daga Fitowa Zuwa Zubewarsu

Likita ina tambaya ne a kan shekarun da mutum zai kai kafin hakora su kammala fitowa a bakinsa. Me ya sa lokacin da hakoran karshe…

Taswirar hakoran babban mutumLikita ina tambaya ne a kan shekarun da mutum zai kai kafin hakora su kammala fitowa a bakinsa. Me ya sa lokacin da hakoran karshe ke fitowa a bakin mutum wajen ke zafi, har ma ba a iya tauna abinci? Shin ko akwai wani maganin da za a yi amfani da shi wajen magance ciwon yayin fitowar hakoran karshen?
Amsa: To idan aka dauki bayani dalla-dalla, likitocin hakora sun tabbatar da cewa hakora dai tun jariri na ciki ake fara samar da su, sa’annan sai su yi zamansu cikin dasashi kafin su fara fita fili a bakin jariri tun daga watanni shida na haihuwa, a wasu ma tun a wata na hudu, a wasu kalilan kuma sai bayan wata tara, kai wasu ma da hakoran nasu suke zuwa duniya.
A mafi yawancin lokuta na gaba guda biyu ne ke fara fitowa a kasa kafin na sama, sa’annan sai na saman, sa’annan bayan wasu makonni na gefensu su fito su ma kasa kafin sama. Amfanin wadannan shi ne, yankawa da gutsurar abinci. Daga nan sai fika masu tsinin nan na gefe dama da hagu, sama da kasa, wadanda ake amfani da su wajen huda abinci. Daga nan sai kananan turame, wadanda ke taimakawa aikin tauna abinci. Dukansu dai sukan kai shekaru biyu ko biyu da rabi kafin su gama fitowa, daga nan sai a ce hakoran yarinta sun cika ke nan. Dukkansu guda ashirin ne a wannan lokaci, goma a sama, goma a kasa.
Daga shekaru biyar zuwa shida kuma sai yara su fara famfara, wadda ke nufin zubar da su wadancan hakora ashirin ke nan gaba daya amma daya bayan daya, ana maye gurabensu da sabbi masu kwari da girma. Zuwa dai shekaru sha biyu ya kamata a ce an gama famfara. Akwai wasu yara kalilan har ila yau da ba su famfara a wadannan shekaru sai can bayan sun kara girma. A wasu kuma ko an yi famfarar, kafin wasu sabbi su fito sai an dauki lokaci mai tsawo. A al’adu da dama, akan fada wa yara zantuttuka na raha domin kada su damu lokacin famfara. Misali, a hausance akan ce musu kada su yi dariya a gaban kadangare don kada ya ga gibinsu. A kasashen Turai akan ce wa yara idan hakorinsu ya fadi su dauka su boye domin za su sami kudi, da dai sauransu. Sa’annan babu kamshin gaskiya a kimiyyance na cewa kadangare kan iya sa irin wannan jinkirin fitar sabbin hakora. A kimiyyance sai dai ko rashin sinadaran calcium da bitaman na rukunin D.
A wadannan shekaru na famfara ne wato tsakanin 6 zuwa 12 manyan turame biyu-biyu a kowane gefe da sama da kasa ke bullowa, wadanda su da can ba su bullo ba, wato su ba a yi musu famfara ke nan, idan suka zube da wuya wasu su sake fitowa. Bayan kamar shekaru 8 kuma wato zuwa shekaru ashirin su manyan turame na can karshen kowane bangare sukan fito. A wasu sai sun doshi talatin ma kafin su fito. To ka ji. Lissafin hakora ya tashi 32 cif ke nan. Kowane gefe kamata ya yi akwai takwas, dama da hagu, sama da kasa.
Kamar yadda ka ji an ambata, bayan famfara babu wata kuma famfarar ta biyu, wato babu wani hakori da zai fadi a ce wani sabo ya bullo, sai dai a sa na asibiti, shi ya sa ake son tattalin hakora ta hanyar tsabtace su akalla sau biyu a kowace rana, da kuma zuwa ganin likitan hakora akalla sau daya a shekara koda ba su ciwo, domin wankin asibiti.
Can idan shekaru sun ja da yawa kuma ga wadanda suka kai lokacin, akan fara samun fitar hakora na tsufa, koda su hakoran ba su mutu ba. Ainihin jijiyar hakoran ce take fara saki a wadannan shekaru. Yawan hakoran da suka rage a tsufan mutum ya danganta da irin kulawa da yake da su a kuruciya, da samun abinci mai gina jiki mai sinadarin calcium, da kuma ilminsa. Sai kuma busa sigari, domin masu shan sigari sun fi samun saurin mutuwar hakora.
Game da bangaren tambayar ta biyu kuma wajen zafin fitar hakori, haka ne idan hakora suka zo bullowa daga dasashi akan iya samun ciwo da dan kaikayi, a yara ma har da zazzabi a wasu lokuta. Shi ya sa za a ga yara masu sabbin hakora suna yawan kuka da furzar miyau don su sosa wurin. dan Panadol zai iya kashe radadin. Akan iya ba manya ma wadanda babban turminsu zai fito wannan Panadol domin kashe zogi. Duka wannan zogi da zarar hakora sun gama fitowa yake tafiya, ba za a sake jin shi ba. Duk wani ciwon hakori kuma bayan wannan zai iya nuni da cinyewar hakorin kuma yana bukatar zuwa ganin likitan hakori cikin gaggawa. A yanzu ba kamar da ba, akan iya ganin ’yan kananan asibitocin hakori na kudi a cikin birane duk da na hukuma ya yi karanci.
Ni kuma so nake na san me zan yi fuskata ta dan ciko, saboda duk na rame ta fuska kuma ni ba rashin lafiya na yi ba. Ka huta lafiya.
Daga Ahmad Lawan
Amsa: Akwai lokutan da mutum zai ji irin haka musamman idan samartaka ta zo, ko yana aikin karfi, ko yana motsa jikin da ya wuce kima. Idan ka lura kusan duka jarirai fuskarsu cike take da kumatu amma suna girma suna kara shekaru, jiki da fuska su kuma kara motsewa suke.
Idan ka ce kuma rama ce, to sai a yi tunanin ciwo. Amma in dai ciwo ne yawanci ramar tana hadawa da jiki baki daya, amma in dai a fuska ce kawai ba za a ce kai tsaye akwai wata matsala ba. Yawanci masu aikin karfi sukan kara jiki da damtse amma fuska sai ta motse. Wannan ba wata matsala ba ce.  Abin da za ka yi shi ne, ka samu ka nemi wani asibiti ka je ka ga likitan kwarai ka fada masa matsalar domin a auna ka a tabbatar ba cuta kamar yadda ka ce, sa’annan za a ce maka ba matsala.
Idan ma kuma abin damuwa yake sa maka, to ya kamata ka daina damun kanka, musamman idan ba mutane ne ke ce maka fuskarka na kara fadawa ba, domin wasu kuma da dama suna nan kumatu ya cika musu fuska suna so su rage.
Wasu za su iya ba ka shawarar shan magungunan nan masu sa jiki ya fashe da kiba, amma mun sha fada hakan bai dace ga lafiyarmu ba, don haka kada ka dau irin shawarwarinsu.

LAFIYAR MATA DA YARA

Sinadaran Da Mai Juna Biyu Ta fi Bukata

A makon da ya gabata mun ga shawarwari domin samun juna biyu. A yau za mu duba sinadaran da mace mai niyyar samun juna biyu da mai juna biyun ma suka fi bukata:
1-Sinadarin Iron: Wannan sinadari shi ne ke da alhakin sarrafa kwayoyin jini, wanda karancinsa kan faru a kowace mai juna biyu. Alamun karancin jini a jiki sun hada da yawan gajiya, yawan faduwar gaba da yawan samun ciwon kai. Ana samun wannan sinadari a nama, kaji, alaiyahu, wake da waken soya. Dole ne a gane cewa mace mai juna biyu (musamman daga wata na uku na daukar ciki zuwa haihuwa da shayarwa) komai yawan cin wadannan kaya da muka lissafa dole sai an kara mata na kwayoyi saboda jaririnta, tunda ko mace mai yin al’ada ma tana bukata a wadannan ’yan kwanakin, ballantana mai juna biyu. Idan ba za ta iya hadiyar kwaya ba, sai a nemo mata na ruwa.
2-Sinadarin Folic acid: Wannan sinadari shi ne ke da alhakin kyautata ingancin dukkan kananan halittun jiki wato cells na jikinmu. Ana samunsa da dama a hanta, kwai, da kayan ganye, wake da kayan marmari. Duk da haka matar da take da niyar samun juna biyu dole ta nemo kuma ta fara shan kwayoyinsa tun ma kafin ta samu juna biyu. Shi ma sinadarin folic acid tun ana amarci mace take fara sha duk da cewa tana samu a abinci. Wannan sinadari yakan rage haihuwar jarirai masu nakasa a jiki, kamar masu yankakken lebe, ko masu cindo, ko masu wata nakasa a gadon baya da dai sauransu.
3-Sinadarin Calcium: Wannan yakan taimaka wa jariri wajen gina kasusuwa masu kwari, kuma ana samun su a madara da kifi. Akwai ma wasu nau’ukan abincinmu da yanzu akan kara wa wannan sinadari. Duk da haka ana so mace mai juna biyu ta sawo kari a matsayin kwayoyi a kyamis ta sha kwaya daya a kullum tsawon watannin cikin.
4-Sinadarin bitaman na rukunin D: Shi kuma wannan ba a ba da shi a asibiti don haka ke za ki nemo shi da kanki. Shi ma akan iya samun shi a abinci kamar su kifi da man kifi da madara. Akwai wanda kuma jikinmu ke sarrafawa daga hasken rana a karkashin fatarmu. Shi ma wannan sinadari dole ne a samu a rika sha domin ya kara taimaka wa sinadarin calcium ne wajen samun kwarin kashi da hakora.
Wadannan su ne muhimmai. Sauran sinadaran bitaman da mai juna biyu kuma ke bukata na abinci ya wadatar.