✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hako man Kolmani: Bauchi da Gombe sun kulla kawancen aiki

Aikin hako mai a Kolmani shi ne irinsa na farko da zai gudana a yankin da ma Arewacin Najeriya baki daya.

Gwamnonin jihohin Bauchi da Gombe sun amince za su yi aiki tare domin tabbatar da nasarar aikin hako danyen mai a yankin Kolmani.

Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da aikin, Gwamnan Bauchi Bala Mohammed, ya ce, duk da dai Rafin Kolmani na kan iyaka ne tsakanin Karamar Hukumar Alkaleri a Bauchi da Karamar Hukumar Akko a Gombe, akwai fahimtar juna a tsakaninsu.

Ya ce, “Za mu ci gaba da mara wa kokarin Gwamnatin Tarayya baya da martaba tsare-tsarenta na kiyaye rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma ci gaban tattalin arziki.”

Shi ma Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya ba da tabbacin jiharsa za ta ba da hadin kan da ya dace a matakai daban-daban domin cim ma nasarar wannan aiki.

Kolmani yankin ne da ke tsakanin Jihar Bauchi da Gombe, inda a nan Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hako mai a ranar Laraba.

A watan Oktoban 2019, Kamfanin NNPC ya ba da sanarwar gano danyen mai da gas Rafin Kolmani.

Wannan shi ne karon farko da aikin hako mai zai gudana a yankin da ma Arewa maso Gabashin Najeriya.