✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hakkokin mata a kan mijinta

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A ci gaba da kawo muku mukalar Albani da muke yi, a wannan makon ga bayani…

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A ci gaba da kawo muku mukalar Albani da muke yi, a wannan makon ga bayani kan hakkoki mata a kan mijinta.
Daga nan kuma sai su ci gaba da tattaunawarsu a matsayin sababbin ma’aurata.
  Amma lallai ne, idan mutum zai sadu da iyalinsa, ya yi kokari ya rika karanta wannan addu’ar: “BISMILLAHI, ALLAHUMMA JANNIBNISH-SHAIdANA, WA JANNIBISH-SHAIdANA MA RAZAkTANA”.
 Ma’ana: “Da sunan Allah, Ya Ubangiji, ka nisantar da ni daga shaidan, kuma nisantar da shaidan daga abin da ka azurta mu da shi.” (Bukhari 5165, Muslim 1434).
Manzon Allah (SAW) ya ce: “idan har Allah Ya kaddara arzikin samun da, to shaidan ba zai shafe shi ba har abada”.
Da ma’aurata za su rika yin wannan addu’ar a kodayaushe, da sun ci nasara a rayuwar aure, ‘ya’ya da zuri’a gaba daya.
(D)    Haramun ne saduwa da mace a lokacin da take cikin jinin haila ko haihuwa, har sai ta yi wanka, idan mutum ya yi hakan (lokacin haila ko haihuwa) ya saba wa Allah (SWT), sai ta yi tsarki, ta yi wanka sannan ya sadu da ita, Allah (SWT) yana cewa: “Matayenku ai gonakinku ne, ku je musu ta ko’ina kuke so (inda Ya dace)” (Bakara 223). Wato ta ko’ina mutum zai iya yi, amma ban da ta dubura, don yin haka luwadi ne, kuma haramun ne, hanya ta la’ana, kuma haramun ne bayyana asiran saduwa da iyali, Manzon Allah SAW ya ce: “Duk wanda ya yi haka shi ne mafi ashararan mutane ranar alkiyama” (Muslim 1437, Abu Dawud 4870).
Idan aka kiyaye wadannan za a samu albarkar aure insha Allahu.   
Hakkokin mace a kan mijinta:
Wadannan hakkokin kiyaye su shi ne kashin-bayan tabbatuwar aure da ni’imarsa, rashin kiyaye su kuwa babbar matsala ce. Ga su nan kamar haka:
(1)    Samar mata da wurin zaman da ya dace don kare mutuncinta, kamar yadda Allah (SWT) Ya ce: “Ku zaunar da su a inda kuke zaune gwargwadon samunku” (dalak 6).
(2)    Dole ne ya sama mata abinci gwargwadon karfinsa, kamar yadda Allah (SWT) Ya ce: “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuma aka kuntata masa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi” (dalak 7).
(3)    Ya tufatar da ita a lokacin da ya dace, gwargwadon halinsa, Manzon Allah SAW ya ce: “Ka tufatar da ita, idan ka tufatar da kanka.” (Abu Dawud 2142, Ibnu Majah 1850).
(4)    Biya mata bukatarta ta ‘ya mace wannan dole ne, gwargwadon yadda Allah (SWT) Ya halicce su, haka zai taimaka wajen tsare mata mutuncinta, kuma hakki ne babba, kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake cewa:  “Lallai ga iyalinka akwai hakkinta a kanta” (Bukhari 1977, Muslim 1159). Duk wanda yake tare da matarsa, har ya kaurace mata tsawon wata 4 babu saduwa, sai ta yi kararsa wajen magabata, ko ya sake ta, ko ya dawo ya gyara hali, wannan ai cutarwa ce babba.
    (Wannan shi ake kira Iyla’i, kamar yadda ayoyin Bakara suka yi bayani, duba bayanin malamai a cikin ‘Alfikhu Alal Mazahibil Arba’ah’ na Abdurrahman Aljuzairy).
 
(5)    Dole ya karantar da ita yadda za ta bauta wa Allah (SWT), ko dai ya yi da kansa ko ya roki wani, ko ya dauki nauyin hakan. Rashin koya mata addini hadari ne babba, don kusan duk tarbiyyar gidan a hannunsu take, idan ba su san addini ba, ’ya’yansu za su tashi a lalace, sai dai wani ikon Allah. Koyar mata addini shi ne kare kai da iyalai daga shiga wuta, kamar yadda Allah Ya yi umurni inda yake cewa: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku tsare kanku da iyalanku daga wutar da makamashinta mutane ne da kuma duwatsu.” (Tahrim 6)). Amma koya mata wani ilimi ko sana’a wannan ci gaba ne da samun saukin taimako a rayuwa.
(6)    Kada ya cutar da ita, da duka, zagi, musgunawa da kaskantarwa, don mace tana da daraja a wajen Allah (SWT), duk abin da ya faru sai a bi dokokin da Allah Ya gindaya, kada a bi son zuciya. Hakuri da danne zuciya suna da muhimmanci a cikin al’amuran duniya, ba ma ana aure kawai ba, don haka abin da bai taka kara ya karya ba, bai kamata ya zama bala’i ba.
   Idan mace ta yi laifi har ga Allah, akwai mataki guda 3 kamar haka:
(A)    WA’AZI: Za a yi mata wa’azi na bayanin muhimmancin biyayya da illar saba wa miji ko bala’in saki .
  (B) kAURACEWA: Idan wa’azi bai yi ba sai a kaurace mata a wajen kwanciya, a ki kulawa da ita a cikin dakinta, amma dole ne a ba ta abinci don Annabi SAW ya ce: “kada ka kaurace mata sai a cikin daki.” (Abu Dawud 2142, Ibnu Majah 1850 da Ahmad 4/447).
 (C) DUKA: Daga nan kuma sai dukan ladabtarwa, ba mai cutarwa ba, ban da dukan fuska, ban da zagi ko bakaken maganganu, ba kuma a gaban yara ko a waje ba. Idan abu ya faskara kuma sai a je wajen magabata don su warware matsalar. Wadannan matakai 3 Alkur’ani ne ya ambace su. Duba (Suratul Nisa’I, aya ta 34).
 Wannan shi ne tsari, daga nan kuma, ko a yi sulhu ko a rabu, Allah Ya sauwake.
(7)    Rashin bayyana sirrinta: Haramun ne ya bayyana sirrinta, kamar yadda ita ma aka haramta mata bayyana nasa. Annabi (SAW) ya yi gargadi a kan bayyana sirrin juna, tun da an hadu dole ne kowa ya san asirin kowa.
 
(8)    Lallai ne a ba ta izinin fita idan ya zama dole ko ya kama, don zuwa asibiti, makaranta, gidan iyaye ko na ‘yan uwa, da sharadin rashin aukuwar fitina, idan akwai matsala sai a dauki matakin gyarawa.
(9)    Dole ne ya yi wa matarsa kyakkyawan zato, ban da tuhuma, zargi da dari-dari, idan har akwai shakku to sai ya dauki matakin gyara a zahirance ba a munafurce ba. Allah (SWT) Ya ce: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku nisanci da yawa daga zato, lallai wani sashin zato laifi ne, kada ku yi leken asiri…” (Hujrat 12).
    Shi ya sa Manzon Allah ya ce:   “Idan mutum ya yi tafiya kada ya dawo gida da daddare kwatsam, ba tare da ya sanar da iyalansa ba.” (Bukhari 5244).
Kuma idan mijin mace ba ya nan, idan ya kama a shiga wurinta, to duk wanda zai shiga kada ya je shi kadai, ya nemi wani muharraminta, ko wasu mata, don kauce wa mummunan zargi.
Za mu ci gaba.