A ranar 3 ga watan Nuwamba 2018, Hakimin Gundumar Sabon Garin Zariya Dan Barhin Zazzau a Jihar Kaduna Alhaji Ahmad Bashir Aminu, ya yi wa shugaban Kungiyar Mahauta na Karamar Hukumar Sabon Gari Alhaji Adamu Ibrahim Chigari, rawanin Dallatun Dan Barhin Zazzau. Bayan nadin sarautar ga yadda tattaunawarsa ta kasance da Aminiya inda bayyana burinsa ga al’ummar Gundumar Sabon Gari.
Gabatar mana da kanka?
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, suna na a Adamu Ibrahim Chigari, ni ne Darakta na kamfanin Zariya Suya kuma ni ne shugaban kungiyar mahauta na Karamar Hukumar Sabon Garin kuma ni ne Yariman fawa na abbatuwa, yanzu Allah ya karamin da sarauta wanda Hakimin Sabon Gari ya bani, a matsayin Dallatun Dan Barhin Zazzau.
Wannan Sarautar tana karkashin wace masarauta ne?
Sarautar Dallatun Dan Barhin Zazzau tana karkashin Hakimin Gundumar Sabon Gari ne watau Alhaji Ahmad Bashir Aminu kuma zan yi aiki karkashin ofishinsa.
Wannan sabuwar sarauta da ka samu, mene ne burinka ga al’ummar Gundumar Sabon Gari?
Wannan dai sarautar an bani ne, akan mu zama mataimaka ga shi Hakimin Sabon Gari Dan Barhin Zazzau Gundumar Sabon Gari, saboda aikace-aikacen shi na masarauta ya duba cancanta da yanayin mu’amalolinmu da yadda muke da mutane. Ni burina a wannan sarauta shi ne, mu taimaka ma shi wajen aikin da zai kawo wa ’yan Gundumar Sabon Gari ci gaba, wajen tabbatar da an samu ingantaccen zaman lafiya a Sabon Gari wajen dukkan wani ci gaba da zaizo ta fannin masarauta a Sabon Gari wanda za a kawo wa al’umma ci gaba. In Allah ya yarda zamu bada gudunmawarmu a fannin da za a kawo wa al’umma zaman lafiya a Sabon Gari da yardar Ubangiji zamu bada gudunmawar mu, a fannin da za a kawo matasa ci gaba insha Allahu, za mu yi iya bakin kokarinmu wajen bayar da gudunmawarmu da lokacinmu da kokarinmu wajen samar da dawwamammen zaman lafiya da ci gaba da yardar Allah.
A matsayinka na Shugaban kungiyar mahautan Sabon Gari. Ko kana da wani kira ga mahautan Sabon Gari don bunkasa harkokin kasuwancinsu?
Gaskiya ni babu abin da zan ce wa kungiyar mahautan Sabon Gari sai godiya saboda irin tsarin da kungiyar take tafi da shi, na yadda da yadda suke gudanar da sana’armu ta fawa da kuma yadda ake bin tsarin kasuwanci ya kuma bunkasa, tsakani da Allah mun dauko hanya kuma Karamar Hukumar tana bamu gudunmawa a fannin canji na gyaran kasuwanci, ba zance komai ba sai godiya. Ina yin kira ga mahautanmu na Sabon Gari da su ci gaba da kiyaye doka tun daga dokar Gwamnati har dokar kungiya, mahauta mutane ne masu biyayya, masu kiyaye doka kuma nasan su na kiyaye doka daidai gwargwado domin samun zaman lafiya don haka ina kara kira ga mahautan Sabon Gari har na Jiha da ma na Najeriya baki daya su kiyaye doka. Abi dokar gwamnati a zauna lafiya. Duk abin da aka ce wannan doka ce toh jama’a a yi kokari a kiyaye ta. Don haka nake jaddadawa al’ummar Sabon Gari a zauna lafiya. Idan an kiyaye dokar kungiya sai a kiyaye dokar gwamnati. Saboda ba mu da wani abu a cikin kungiyarmu da ta saba wa Gwamnati, idan har an kiyaye doka za a zauna lafiya.
Akwai masu alakanta nadin Sarauta ga masu mulki ko masu dukiya. Me za ka ce?
Gaskiya masarautu daban-daban ne, kowace masarauta akwai irin abubuwan da take zuwa da shi. Gaskiya mu dai anan Gundumar Sabon Gari wani tunani da jama’a suke yi wai sai ka zama wani ko kuma kana yi wa masarauta hidima sannan zaka samu Sarauta, idan ka samu sarauta ka koma masauta ka tare. Tsakani da Allah wannan ba gaskiya bane. A iya sanina a masarautar Gundumar Sabon Gari akwai mutanen da ba su da komai basu da abin zasu sayi rawani an yi masu nadi. Ko lokacin da aka min rawani akwai wadanda aka yi wa rawani basu da komai, cancantarsu ce tasa aka yi masu rawani, ka ga ko inda kudi ne basu da kudin da zaisa a yi masu rawani a wannan masarauta tamu. Sannan akan batun wai idan an yi maka sarauta ka koma masarsauta ka yi ta masu hidima wannan ba gaskiya bane, ban san wannan abun ba. Kamar ni yanzu tunda aka yi mani wannan nadin nasan dai akwai gaisuwa da ake zuwa a yi wa Hakimi a matsayin shi na uba, wanda nasan ko ’ya ce aka ba ka za kaje ka yi gaisuwar surukai da ake cewa hakama idan aka yi maka sarauta zaka je ka yi gaisuwa. In banda wannan gaisugwar har yanzu ban koma da sunan naje gaishe shi ba, ko tunanin in yi mashi wani abu ba, mai nake da shi da zan yi mashi. Sai dai kawai fannin aikin ofis ko na masarauta idan ta kama ka je. Don haka duk irin wadannan abin da jama’a suke tunani ba dai masarautar Gundumar Sabon Gari ba. Su ma wadancan masarautun da mutane ke tunanin ana haka sai an bincika sai a tabbatar da ba haka ake gudanar harkokin masautar ba. Don haka ina kira ga jama’a su daina farfaganda akan abun da basu sani ba, wanda hakan yake haifar da wasu abubuwa har su rikice, don haka sai a kiyaye saboda ba abubuwa bane mai kyau.