Hakimin Bodor da ke Jihar Gombe, Alhaji Sale Tinka ya zargi shugaban kwamitin riko na karamar Hukumar Funakaye Alhaji Usman Ribadu da tsohon dan Majalisar Tarayya a yankin Alhaji Abubakar Abubakar BD da keta masa haddi da ci masa mutunci a rumfar zabe a ranar zaben gwamnonin da ya gabata.
Da yake shaida wa manema labarai yadda lamarin ya faru a Gombe, Hakimin Alhaji Sale Tinka, ya ce a ranar zaben gwamnoni da ’yan majalisa yana Gombe sai aka kira shi a masarautarsa cewa akwai matsala matasa na zuwa da katunan zabe masu yawa suna cewa dole a tantance su, don haka ya bar Gombe ya tafi.
Hakimin ya ce, a hanyarsa ya tsaya a wani kauye da ake kira Garin Gidado, don jin abin da ke faruwa, inda a nan ne aka gaya masa cewa matasa ne suke zuwa da katunan zabe da dama suna cewa lallai sai an tantance su da aka ki shi ne suke son ta da rikici, ya ce da ya hana sai ya wuce fadarsa a Bodor.
A cewar Hakimin, yana zuwa Bodor sai ya tarar da wasu matasa da ya yi musu magana don hana tashin hankali sai wani mai suna Kawu ya fara zaginsa yana cewa zai ci mutuncinsa. “A matsayina na Basarake da na ga lamarin zai baci sai na nemi in bar wurin. Ina kokarin tafiya sai ga shugaban karamar hukumarmu Usman Ribadu da Abubakar Abubakar BD tsohon dan majalisar tarayya sai ji na yi kawai Ribadu ya shake min wuyar riga yana zagina yana cewa sai ya ci mutuncina har ya yaga min wuyar rigar yana cewa mu tafi caji ofis su ga me na taka,”inji Hakimin.
Ya ce bayan zagi da cin mutuncin da shugaban ya yi masa, shi ma Abubakar BD ya zage shi yana cewa idan rashin mutunci yake ji yanzu aka fara su zuba su gani.
Ya ce su Sarakuna ba sa siyasa su ’yan siyasar ne ke tilasta musu shiga siyasa har suke yi musu barazanar duk Basaraken da bai kawo rumfar zabensa ba za a tube shi.
Ya ce sai daga baya ya gane cewa matashi Kawu da ya ci masa mutunci ashe wai so yake yi a cire Sarkin Bodor din daga Hakimci a ba shi Dagaci.
Da wakilinmu ya tuntubi Ciyaman din Usman Ribadu don jin ta bakinsa, sai ya ce ba zai ce komai ya je ya tambayi Abubakar BD da shi ne Sarkin Bodor din ya yi rikici, shi ya yi kokarin tura Sarkin a mota ne. Ya ce sun samu Hakimin ne yana gaya wa mutanen kauyen cewa kada su zabi PDP su zabi APC.
Da manema labarai suka samu Abubakar BD a gidansa, sai ya ce ba zai gansu ba zai tafi gidan gwamnati ne domin yana da taro, kuma da aka sake gaya wa shi Ribadu abin da Abubakar BD ya ce sai ya ce su rabu da shi su je su rubuta labarisu kawai.