✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hakimi mafi dadewa a tarihin Kano, Adnan Mukhtar, ya rasu

Marigayin dai yana daya daga cikin wadanda suka nada Sarakunan Kano 4.

Sarkin Ban Kano, basarake mafi dadewa a tarihin Kano kuma Kwamishinan Ilimi na farko a Jihar, Alhaji Mukhtar Adnan, ya rasu.

Marigayin, wanda daya ne daga cikin masu zaben Sarki a Kano, kuma ya nada Sarakuna har guda hudu, ya rasu yana da shekara 95 a duniya.

Wasu majiyoyi da ke da kusanci da iyalan mamacin sun ce basaraken, wanda kuma shi ne Hakimin Danbatta ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a., kamar yadda wani dandali a zauren sada zumunta na Facebook mai suna ‘Danbatta Youth Group’ ya sanar.

Tarihi dai ya nuna cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ne nada shi a matsayin Sarkin Bai a shekarar 1954, inda ya gaji mahaifinsa.

An haife shi a shekarar 1926, kuma ya halarci makarantar Elementary ta Danbatta, sannan ya halarci makarantar Middle ta Danbatta kafin daga bisani ya wuce makarantar Clerical da ke Zariya.

Ya fara aiki da ma’aikatu daban-daban, kafin a daga likafarsa zuwa Sarkin Bai.

Marigayi Mukhtar Adnan ya kuma taba zama mamba a Majalisar Wakilai Ta Tarayya a jamhuriya ta farko, sannan aka nada shi Kwamishinan Ilimi na farko a shekarar 1968.

Marigayin dai shi ne Hakimi mafi dadewa a tarihin masarautar Kano.

Ya shafe shekara 33 a matsayin Hakimi, Kansila da kuma mai nada sarki.

Yana daga cikin mutanen da suka nada Sarkin Kano Muhammadu Inuwa (1963), da Ado Bayero (1963-2014) da Muhammad Sanusi II (2014-2020) da kuma Sakin Kano mai ci, Aminu Ado Bayero a shekarar 2020.

Wata majiya daga iyalan mamcin ta shaida wa Aminiya cewa za a yi jana’izarsa ranar Juma’a, ko da yake ba a sanar da takamaiman lokaci ba.