A makon jiya ne aka samu motsin kasa a sassan Abuja, lamarin da ya firgita mutane. Aminiya ta zanta da wani masanin ilimin kimiyyar muhalli a sashin yanayin kasa (Geography) na Jami’ar Abuja, Farfesa Hassan Shu’aibu Musa inda ya ce wasu ayyuka na dan Adam ka iya haddasa girgizar kasa. Ya kuma yi bayani kan darasin da ya kamata hukuma ta koya a kan motsin kasa da ya auku a Abuja.
Mene ne bambancin girgizar kasa da motsin kasa da aka fuskanta a yankin Abuja?
Bisa ga al’ada girgizar kasa tana farawa ce da motsawarta, idan motsawar ta kai ga girgiza sosai sai kasa ta dare, gine-gine da ke kanta su nutse. Haka na faruwa ne dalilin gujewar tsananin takura daga cikin kasa zuwa wajenta a dalilin aikace-aikacen dan Adam ko kuma wanda yanayi ya samar. Idan lamarin ya yi muni shi ne yake kaiwa ga girgizar kasa. Sai dai wanda aka fuskanta a yankin Mpape inda ake fasa duwatsu soasai da wasu wurare da ke makwabtaka da garin, ya tsaya ne a matakin motsi, bayan wani lokaci sai ya kau ba tare da ya kai ga matakin darewar kasar ba.
A kimiyyance ko akwai wasu ayyuka na dan Adam da za su iya haddasa haka?
Duk abin da za mu fada yana matsayin hasashe ne kawai saboda na farko Abuja na kan yanki ne na daidaitacciyar kasa, ba ta kan layin duniya da kasa ta rabu gida biyu inda a can ne kimiyya ta nuna za a fuskanci matsalar. Sai dai bisa ga la’akari da garin Mpape, sananne ne cewa yanki ne da ke kewaye da tsaunuka wadanda daga jikinsu ne ake yawancin aikin duwatsu don amfani da su wajen gina gidaje da tituna da gadoji a nan Abuja, ciki har da tsakuwar da a ke samu a yayin fasa duwatsun. Haka lamarin yake a sauran wurare da ke kusa da wurin inda a can ma ake taba ayyukan. Wani abu da ka iya haddasa wannan matsalar kuma shi ne hakar rijiyoyin burtsatse ba kan gado. Kusan duk wani gida a birnin Abuja kasaitarsa bai kammaluwa sai an tona masa rijiyar burtsatse na kansa. Sannan yawancin rijiyoyin burtsatsen nan da ake haka ana yinsu ne irin na masana’antu masu zurfin gaske da hakan ka iya ba da kafar kubucewar takura daga karkashin kasa zuwa wajenta.
Wane mataki kake ji hukuma za ta iya dauka don magance aukuwar girgiza da ayyukan dan Adam ka iya haddasawa?
Dole a gindaya dokoki a kan ayyukan hakar rijiyoyin burtsatse da na fasa duwatsu. Ya zama sai an ba da izini a haki rijiyar sannan mai nau’i kaza idan har ya zama dole sai an yi rijiyar. Sannan ta fuskar fasa duwatsu a takaita aikinsa ga masu lasisi kawai da kuma irin girman nakiyar da ya kamata a yi amfani da ita da kuma wuraren da aka amince a gudanar da aikin ba ko’ina ba.
Ko akwai wata illar da hakar rijiyar burtsatse ka iya haddasawa?
kwarai kuwa yawaitar rijiyoyin burtsatse na shafar tsirran da ke kan kasa, saboda kullum tana tsotse ruwan da ke karkashin kasa na nesa daga tushen mabubbugarsa. Ka ga a kwana-a-tashi sai ya shafi na saman wanda zai haddasa mutuwar tsirrai. Sannan idan aka lura da adadin ruwan sama da muke samu da wadatar tsirrai ke ingiza wanzuwarsa ya ja baya sosai a yanzu a kan na shekarun baya. Kuma tushensa shi ne kafewar ruwan da ke karkashin kasa sakamakon hakar wurare masu dausayi da ake yi kullum. Haka ya kamata a san samfurin ruwan da ke cikin rijyar gudun ko tana dauke da wani nau’in ma’adini da ka iya lahanta lafiytar mutum
Kana jin rafukan da muke da su a kasar nan za su iya samar da ruwan da ake bukata don tacewa da amfanin jama’a ba tare da yin rijiyoyin nan ba?
Ba lallai ne su wadatar ba, sai dai akwai wasu hanyoyi na daban da za mu iya amfana da su don samar da ruwan bukatunmu. Sun hada da adana ruwan sama a gidaje da garuruwa wanda sinadari kadan ne yake bukata don aiwatar da haka. Za mu kuma iya adana shi ne ta hanyar tararsa maimakon barinsa da ake yi yana ta tafiya a kasa haka nan. Akwai wurare da dama da na sani da ake yin haka da suka hada da Jihar Imo tun lokacin da na yi hidimar kasa.