✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajiya Zara Goni

Hajiya Zara Goni: Burina in ceto matan Najeriya Hajiya Zara Goni haifaffiyar garin Maiduguri ta Jihar Barno ce, tana da shekara 42, ta yi digirinta…

Hajiya Zara Goni: Burina in ceto matan Najeriya

Hajiya Zara Goni haifaffiyar garin Maiduguri ta Jihar Barno ce, tana da shekara 42, ta yi digirinta na farko a jami’ar Maiduguri, inda ta karanta ilimin kimiyya (science education). Ta yi digiri-na-biyu har biyu a kasar Indiya, inda ta karanta Tsarin Kula da Ma’aikata (Human Resource Planning) da kuma Harkokin kasashen waje (International Relations). Ita da kawarta suka kafa kungiyar NGO mai suna Gabasawa Women and Youths Empowerment Initiatibe wadda ke Jihar Legas. Suna taimakawa mata, yara da kuma matasan arewa da ke Jihar Legas.

Tarihina
Sunana Zara Binta Goni, shekaruna 42. Na yi karatu a jami’ar Maiduguri (Unimaid), na karanta ilimin kimiyya (Science Education). Na yi digiri-na-biyu a kan huldar kasashen waje (International Relations),na kuma yi digiri-na-biyu a kan Tsarin kula da ma’aikata (Human Resource Planning and debelopment). Na fara aikin gwamnati a 1996, daga nan sai na fara aiki da kungiyoyin NGO. Ina taimaka wa talakawa da kuma yadda mutane za su tafiyar da al’amuransu. Na yi aiki wurin sasanta rikici ko kawo maslaha (conflict management) kuma har yanzu a wannan aikin nake. Ni da kawata muna da kungiyar NGO mai suna Gabasawa Women and Youths Empowerment Initiatibe a Legas, amma ni ke tafiyar da ta arewacin Najeriya. Muna kulawa da ‘yan arewa a Legas, inda muke ba su shawarwari a kan irin sana’o’in da ya kamata su yi.
Burina da nake karama
Da nake karama mahaifina ya so na zama likitar dabbobi, amma da na fara sai na ga ya yi wahala kuma ba zan iya ba. Sai na karanta tsarin kula da ma’aikata, kasancewar ina da sha’awar karanta shi, kuma sai gwamnati ta ba ni gurbin karatu zuwa Indiya. Ina sha’awar in ga na sanya zaman lafiya a tsakanin matasa da kuma hana su shiga gurbatacciyar kungiya.

Shakuwa tsakanin iyaye
A gaskiya na fi shakuwa da mahaifina, saboda yakan ba ni shawarwari da dama wadanda suke taimaka mini wajen tafiyar da al’amurana.
Abin da na koya daga iyayena
Iyayena masu natsuwa ne, sun nuna mana komai kake so a rayuwa Allah Zai taimake ka ka samu idan ka yi kokari da kuma kwazo. Sun koyar da ni yadda zan zama mai kwazo wajen gudanar da aikina. Mahaifina ya gaya mana a kullum mu kasance masu mayar da hankali a kan karatu, na kur’ani da na boko don su ne za su zama mana mafita a duniya. Duk da ma mahaifin nawa ya tsufa yanzu, amma har yanzu muna bin tafarkin tarbiyyar da ya koyar da mu tun a da.
kalubalen da na taba fuskanta wajen gudanar da aiki
A gaskiya na fuskanci kalubale da dama. Domin na taba aiki a yankin Neja-Delta, kuma na yi aiki a kowace jiha a Najeriya. A gaskiya samun yardar mutane musamman ma wadanda ba su taba sanin ka ba yana da wuya. Muna aiki da unguwanni daban-daban a kowace jiha. Kuma kafin ka samu  yarda daga wajensu da kuma abin da kake so su fahimta akwai wahala. Amma kasancewar mun yi hakuri sannan ga taimakon Allah, sai muka cim ma burinmu.
Yadda muke taimaka wa mata da matasa
Aikin namu ya shafi mata da yara da kuma matasa. Abin da muke yi shi ne, muna ilimantar da su yadda za su zama masu amfani wurin taimaka wa kasarmu, muna koya musu aikin hannu. Mukan kawo tsare-tsare daban-daban wadanda suke bude musu ido domin su gane  cewa nan gaba za su samu riba da kuma sanin irin aikin da za su yi idan sun tashi yin aiki. Kamar yanzu, mukan canza irin tunanin matasa. Mukan sanya su a aji mu ilimantar da su a kan irin aikin hannu da za su yi don su zama masu amfani a kasarmu Najeriya. Muna da masana wadanda ke ilmantar da matasa a kan yadda tsarin addinin musulunci yake. Da kuma yadda musulunci ya koyar da kwanciyar hankali ba tashin hankali ba.
Mukan ba iyaye musamman mata shawarwari yadda za su rika lura da ‘ya’yansu, kasancewar ‘ya’ya na girmama iyayensu mata sosai, saboda haka, muke sanya iyaye mata a cikin tsare-tsarenmu domin su ne suka fi dacewa su yi wa ‘ya’yansu magana.
Nasarata
Za ki iya samun nasara idan har kika tsaya kai da fata a kan abin da kika sa a gaba. Kuma za ki yi kokarin cim ma burinki a kan abin da kika sanya wa ranki za ki ci nasara a kai. Idan kika ci nasara, ke da kanki za ki ji lallai kin cim ma burinki kuma kin yi nasara. Kamar ki shiga unguwa ki tara mata sai ki rika ilimantar da su a kan wani abu. Bayan wadansu shekaru sai ki ga sun fahimta har su rika bayyana yadda ya kamata wani abu ya zamo wannan shi ne nasara.
Abubuwan da nake sha’awar yi lokacin hutu
In dai na samu lokaci, a gaskiya ina son tafiye-tafiye. Ina son zama cikin mutane domin na ji ra’ayoyinsu game da abubuwa da dama wadanda suka shafi rayuwarsu. Saboda haka, nakan so na yi tafiya don kara ilimi.

Inda na fi sha’awar zuwa
Ina son zuwa Maiduguri, domin idan na je Maiduguri ina ji a jikina a kan cewa na dawo gida kuma ina ganin ‘yan uwana. Duk da yadda garin ya zama ina sha’awar zuwa Maiduguri. Domin an ce duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi.
Wanda nake sha’awar haduwa da shi
Ina sha’awar haduwa da Winnie Mandela. Domin mace ce mai hakuri, kuma ina son idan na gan ta a yau in tambaye ta a kan yaya ta ji da aurenta ya mutu?
Halayen mace da ke burge ni
Macen da ke burge ni ita ce wacce ba ta dogara ga abin da namiji zai ba ta kawai, mai neman na kanta, wadda za ta nema wa kanta komai da kanta ba sai ta jira maigida ba, wadda maigidanta da iyayenta za su yi alfahari da ita don irin yadda take taimaka musu. Mace mai hangen nesa, mai tunani da sanin ya kamata da kuma mai ilimi a fannin addininta da kuma na boko. Wannan ita ce irin macen da ke burge ni.
Tufafi
Ina son doguwar riga, ina son in ga mace ta sanya doguwar riga da mayafi.
Kayan koli
Ina son dogayen ‘yan-kunne, saboda dogayen ‘yan kunne na sanya fuskar mace ta fito su kuma kara mata dogon wuya. Ina sha’awar azurfa sosai.
Shawara ga matasa
Shawara da zan ba matasa musamman ma na Maiduguri ita ce, su yi hakuri. Ina son kowa ya yi hakuri. Saboda a Maiduguri muka girma, gaskiya babu inda ya kai Barno zaman lafiya. Na tuna lokacin da mahaifiyata za ta je wajen kanwarta. Sai ta kulle mu a mota, ta ba wani mai sayar da lemu tsaronmu. Har yakan ba mu lemu mu sha. Har ina sha’awar yadda za a sake ajiye mu wajen mai lemun don ya ba ni lemu. Amma sai aka wayi gari mutane da dama ba su sha’war zuwa Maiduguri. Gaskiya abin yana sanya ni bakin ciki. Mutanenmu masu son kwanciyar hankali ne. Ina ba su hakuri su ajiye bindigoginsu domin dawowar kwanciyar hankali a jihar.
Burina
A gaskiya ina so idan aka yi magana da kowace mace ‘yar Najeriya, musamman ‘yar arewacin Najeriya, tace na taba rayuwarta ta hanya mai kyau. Ko na ilimantar da ita. Ko ta ba da misali da ni, ta ce “akwai ranar da muka yi magana da Zara, inda ta ce a yi haka, kuma saboda hakan, na zama mutumiyar kaina”. Ina son mutane su tuna da ni a matsayin wadda ta taimaka wa mata da yara da matasa ta hanyar samun nasara ga rayuwar zamantakewar yau da kullum.
Shawara ga mata
Ina so mata mu tashi mu taimaki juna. Kuma wadanda suke da ‘ya’ya su tabbata sun ilimantar da su daidai karfinsu. Iyaye su kasance masu ba ‘ya’yansu tarbiyya tagari wadda zai sa su ci nasara a rayuwa da kuma zama abin alfahari a gare su, saboda in an ga ‘ya’yan za a ce ai ‘ya’yan wane ne.