Hajiya Talatu Ahmed tana da zaune a garin Bauchi, ta rike shugabar makaratun sakandaren ’yan mata da ke Nabardo da Kafin Madaki da ke Jihar Bauchi, a yanzu Babbar Darakta ce a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi. Ta tattauna da wakilinmu, inda ta yi bayanin kan gwagwarmayar da ta yi wajen koyarwa, sannan ta ba mata shawarwarin da idan suka yi amfani da su za su gudanar da rayuwarsu cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Daga Hamza Aliyu, Bauchi
Tarihin Rayuwata
Sunana Hajiya Talatu Ahmed, an haife ni a garin Gombe a shekarar 1959, na yi makarantar firamare a Bolari da ke Gombe, daga nan na yi Kwalajen ’Yan Mata ta Gwamnati a Bauchi, bayan na kammala makaranta sai na yi aure a 1981, daga bisani na sake komawa makaranta. Bayan na kammala karatu a makarantar BACAS da ke Bauchi sai na tafi Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda na yi digiri a fannin tarihi, cikin ikon Allah bayan na kammala ABU sai na samu aikin koyarwa, da ma babbar bukatata a rayuwa ita ce in zamo malamar makaranta, kuma Allah Ya cika mini burina.
A shekara ta 1987 na fara koyarwa a makarantar Gobernment Day Secondary School, inda na ci gaba da karantarwa a fannin tarihi, bayan wata tara sai aka canja mini wurin aiki zuwa makarantar barikin sojoji da ke Shadawanka a Bauchi, kuma na yi aiki na tsawon shekara uku a makarantar.
Daga bisani na yi aiki a ma’aikatar ilimi a Jihar Bauchi na wani lokaci, bayan haka na yi koyarwa a garin Nabardo na tsawon shekara hudu, daga nan aka sake tura ni aikin koyarwa a garin Kafin Madaki da ke yankin karamar Hukumar Ganjuwa na tsawon shekara biyu da rabi. Sannan na yi aikin koyarwa a karamar Hukumar Alkaleri a makarantar mata na tsawon shekara uku, daga Alkaleri sai aka sake tura ni zuwa Nabardo. Na yi aiki a makarantar GGSC na tsawon shekara hudu kuma ina da ’ya’ya biyu a halin yanzu.
Mukaman da na rike
Daga shekarar 2000 zuwa 2004 na rike mukamin Shugabar Makarantar ’Yan mata ta garin Nabardo, a karamar Hukumar Toro, daga 2004 zuwa 2007 na rike Shugabar Makarantar ’Yan mata na garin Kafin Madaki da ke karamar Hukumar Ganjuwa, sannan daga 2007 zuwa 2009 aka sake tura ni a Makarantar ’Yan mata a garin Nabardo a matsayin Shugabar makarantar. Daga 2010 zuwa 2011 na rike mukamin Shugabar Kwalejin Gwamnatin ’Yan mata (GGC) da ke Bauchi. Daga 2011 har zuwa yau ina rike da mukamin Babbar Darakta a Ma’aikatar Ilmi a Jihar Bauchi.
Ilimin mata
Kusan a kullum idan muka zauna muna hira da ’yan uwa mata, abin da nake fada shi ne, babu wata al’ummar da za ta samu ci gaba mai amfani sai da ilmi, domin shi ne gishirin zaman duniya. Idan uwa tana da ilimi za ta taimakawa ’ya’yanta ta yadda za su ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsu. Kuma idan ka duba sosai kashi 85 cikin 100 na maza ba sa son aurar wacce ba ta iya karatu da rubutu ba. A yanzu abin da yake bata mini rai shi ne tun lokacin da aka fara tashe-tashen hankula a jihohin Arewa maso Gabas malamai da dalibai suka fara fuskantar koma baya, ta fannin ilmi domin kusan abubuwa sun tsaya cak, kowa hankalinsa ya tashi saboda matsalar tsaro. Amma duk da haka ina kira da babban murya ga hukumomi su taimaka wa wadannan ’ya’ya mata domin su samu damar ci gaba da karatunsu kamar yadda suka saba. Burina
Babban abin da na fi bukata a rayuwata shi ne in ga ’ya mace ta yi karatun boko da na addini, domin ilimi shi ne gishirin zaman duniya. Kuma ina fata ’yan uwa mata za su ci gaba da ba ’ya’yansu goyon baya domin su samu ilmi, ta yadda za su gudanar da rayuwarsu cikin tsari nan gaba.
kalubale
A gaskiya lokacin da nake karatu babu wani kalubale da na fuskanta, tun daga makarantar sakandare har zuwa lokacin da na shiga jami’a, kuma maigidana ya ba ni dukkan gudunmawar da ta kamata, domin ya san mahimmancin ilmi a rayuwar dan Adam. Tsarin makarantu irin na da sun sha bamban da na yanzu, a lokacin da muke karatu dalibai kadan ne, saboda masu son karatu ’yan kadan ne, ba kamar yanzu ba. Dole sai kowa ya bada gudunmawarsa kafin a samu ci gaba a tsakanin wannan al’umma.
Aure ba ya hana karatu
Akwai jama’a da dama da suke cewa aure yana hana karatu, masu wannan tunani sun yi kuskure, domin aure ba ya hana karatu, karatu kuma ba ya hana aure, idan yarinya ta samu wanda za ta aura, abin da ya kamata a yi shi ne, a yi mata aure, sannan ta ci gaba da karatunta a gidan mijinta, kamar yadda aka yi mini aure, sannan na ci gaba da zuwa makaranta. Kuma babbar bukata a rayuwa ita ce in ga ’ya’ya mata sun yi ilimin addini da na zamani. Akwai da yawa daga cikin mata da suke ganin wai sun tsufa ba za su iya karatu ba, muna da makarantun yaki da jahilci a jihohi daban-daban na Najeriya, saboda haka lokaci ya wuce da za mu zauna ba mu da wani aiki sai girke-girke. Mijina ya bada goyon baya dari bisa dari domin in samu damar ci gaba da karatuna.
Bambanci ilimin da da na yanzu
Akwai bambanci sosai tsakanin tsarin ilmin da da na yanzu. A shekarun baya babu batun magudin jarrabawa a tsakanin dalibai, amma yanzu idan ka duba za ka ga malami yana cikin koyarwa a aji dalibi ya bude wayarsa yana bincike a kafafen yada bayanai na zamani. Kuma a da na yi karatun ne tsakani da Allah, amma yanzu abubuwa sun rikice. Idan ka duba kadan ne daga cikin dalibai suke bincike a dakunan karatu. Magudin jarrabawa ya shafi dukkan bangarorin Najeriya, muna fata hukumomi za su tashi tsaye domin magance wannan matsala ta satar jarrabawa. Wayoyin salula sun bada gudunmuwa sosai wajen lalata tarbiyyar yara, domin a fahimtata sharrin ya fi alherin yawa, saboda haka ya kamata iyaye su rika sa ido sosai game da wayoyin da ’ya’yansu suke rikewa. Idan ka duba akwai da yawa daga cikin ’yan mata ba su da wani aiki, sai kwalliya wacce take son karatu na gaskiya ba ta da lokacin yin kwalliya sai ta kammala karatunta.
Tufafi
Akwai wasu daga cikin mata da suke ganin matukar ba su sa tufafi da ba zai bayyana surar jikinsu ba, to ba su burge ba. Duk matar da take wannan shiga to tabbas rayuwarta tana cikin hadari. Da wahala ka ga mace ta sa hijabi an yi mata fyade, saboda ta rufe jikinta, don haka ina ba mata shawara mu ji tsaron Allah, mu gyara halayenmu. Akwai wasu daga cikin iyayen da suke daure wa ’ya’yan gindi, kuma babu wani mutumin kirki da zai auri wacce take nuna tsaraicinta a tsakanin al’umma.
Sakona
Babban sakona ga al’umma shi ne, ya kamata mu ci gaba da addu’oin Allah Ya kawo mana karshen wannan masifa da ke faruwa a jihohin Arewa maso Gabas, wadda ta yi sanadiyyar lakume rayuka dimbin al’umma. An kashe mata, an kashe yara kanana, kowa yana zaman dar-dar ne, kuma abin ya wuce duk yadda mutum yake tsammani, sannan ina kira da babban murya ga mazaje, don Allah duk wanda yake zaune da mace daya ya taimaka ya kara daya. Masu mata biyu su kara su zamo uku, masu uku su kara su zamo hudu, domin zawarawa sun yi yawa sakamakon wannan rikice-rikice a jihohin Arewa maso Gabas. Ya kamata iyaye su rage dogon buri, idan mutumin kirki ya zo auren ’yarsu su tausaya masa, kada a wahalar da shi, tabbas duk wanda yake zaune a cikin garin Bauchi ya san cewa mata sun yi yawa ba mazajen aure.